Wednesday, September 10, 2025

Menene hukuncin Zihari a Musulunci?
Menene hukuncin yin Zihari a Musulunci?

Menene Zihari?

Zihari shine miji ya kamanta ko ya sifanta matarshi da mahaifiyarshi da wata sifa na jikinsu ko suransu.

Zihari dabi'ace da ta samo asali a lokacin jahiliyan larabawa wadanda ke yi ga matayensu a duk lokacin da suke son rabuwa da su, sai su kamanta su da mahaifiyarsu ko yan uwansu na jini.

Shiyasa Allah madaukakin sarki ya saukar da aya a cikin Suratul Mujadala inda yayi hani da Kuma tabbatar da hukuncin kaffara ga duk musulmin da ya aikata irin wannan mummunar dabi'ar ta jahiliya.

Misalin Zihari shine miji yace wa matarshi "hancin ki irin na mahaifiyata ne" ko Kuma idanuwarki sak irin na mahaifiyata",

Saboda haka duk mijin da yace wa matarsa haka Ko makamancin haka, to yayi Zihari Kuma daga lokacin da ya furta hakan ga matarshi ta haramta a gareshi har sai yayi kaffara.


Yadda akeyin kaffara:

Kaffaran Wanda yayi  Zihari kalar kaffaran Wanda ya kashe rai bisa kuskure ne ko kuma yasha azumin Ramadan da gangan, shine 'yantar da bawa/baiwa ko Kuma Azumin wata biyu a jere wato kwanaki (60) ko Kuma ciyar da miskinai (60).

Allah madaukakin sarki ya kiyaye Mana harsunamu don matsayin Shugaban Halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam.



Tuesday, September 9, 2025

Menene Istibra'i kuma yaya ake yinsa a musulunci?
Menene Istibra'i kuma yaya ake yinsa a musulunci?

Ma'anar Istibra'i:

Istibra'i shine jira domin kubutar da mahaifa daga daukar ciki ko kuma zaman jiran a haife cikin da mace ke dauke dashi bayan tabbatar da samuwarsa.


Yadda ake yin istibra'i:

Yadda ake yin istibra'i shine idan matar da zatai istibra'i tana jinin haila to zata zauna har sai taga jini yazo mata sau uku.

Idan kuma bata ga jini ba saboda kuruciya ko yawan shekaru to zata zauna tsawon watanni uku.

Idan kuma tana da ciki ne to zata zauna har sai ta haifi abinda ke cikikinta.


Dalilan da suke sawa ayi istibra'i 

1. Bauta.

Idan mutum yana da baiwa kuma ya kasance yana saduwa da ita sai ya sayar da ita ga wani mutum daban, to wanda ya saye ta bazai kusanceta ba har sai tayi istibra'i.


2. zina ko fyade

idan namiji ya sadu da mace bata hanyar aure ba, ta hanyar zina ne ko kuma fyade to wajibine tayi istibra'i kafin mijinta ya kusance ta in tana da aure ko kuma kafin tayi auren.


Allah a'alamu.



Monday, September 8, 2025

Wednesday, January 1, 2025

Addu'a Bayan Kiran Sallah
Addu'a Bayan Kiran Sallah

Yin addu'a bayan Kiran sallah sunnah ce mai karfi kamar yadda yazo a cikin hadisin da Jabir bin Abdullah (Allah ya yarda da shi ya ruwaito) Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi Yace: duk wanda ya karanta wannan Addu'ar

"Allahumma Rabba hadhihi-dda` watit-tammah, was-salatil qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wa b`ath-hu maqaman mahmudan-il-ladhi wa`adtahu"  bayan ya saurari Kiran sallah to ceto na ya tabbata a gare shi ranar tashin kiyama.

Fassarar wannan Addu'ar shine: 
"Ya Allah Ubangijin wannan cikakkiyar kira da tsayuwar Sallah, Ka yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) ceto da kuma falala, kuma ka daukaka shi zuwa ga matsayin da ka alkawarta masa". 

Bayan an gama Addu'ar, ana kuma yin salati ga Annabi (S.A.W) da cewa 
“Allahumma salli ala sayyidina Mohamad”.

Article Translation in English Language.

Praying after the call to prayer is a strong sunnah as mentioned in the hadith narrated by Jabir bin Abdullah (may God accept him) The Messenger of God, peace and blessings of God be upon him,  said, “Whoever after listening to the Adhan says, ‘Allahumma Rabba hadhihi-dda` watit-tammah, was-salatil qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wa b`ath-hu maqaman mahmudan-il-ladhi wa`adtahu,’ then my intercession for him becomes binding on the day of resurrection.”

The translation of this dua is: 
“O Allah, Lord of this perfect call and established prayer, grant Muhammad the intercession and favor, and raise him to the honored station You have promised him”.

After the adhan, it is also customary to send salutation upon the Prophet by saying “Allahumma salli ala sayyidina Mohamad”. 
Menene ma'anar sunan Mardiyya?


Sunan Mardiyya daya ne daga cikin sunanayen lakani na Nana Fatima (AS) wanda ke nufin macen da Allah Ya yarda da ita, kuma ya yaba da dabi'unta. 

Ma'anar Mardiyya a luga shine Mai Nagarta, Mai Taqawa, Mai Tsoron Allah, Mai Ibadah Ga Allah. 

Mardiyya suna ne Wanda ya samo a sali daga harshen larabci Wanda ake furtawa da Mardhiyyah ko Kuma Marziyyah.

Ya zo a cikin Alqur'ani a suratul 89:28: Inda Allah Madaukakin sarki ke cewa:

ارجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً

"Ku kõma zuwa ga Ubangijinku, kuna masu yarda da (kanku) da kuma mai yarda da Shi".

Article Translation in English Language:

Mardiyya is one of the nicknames of Nana Fatima (AS) which means a woman whom God approves of, and praises her qualities. 

The meaning of Mardiyya above is Virtues, Pious, God-fearing, Worshiper of God. Mardiyya is a name derived from the Arabic language which is pronounced as Mardhiyyah or Kuma Marziyyah. 

It comes in the Qur'an in Surah Al fajr 89:28, Where Allah Almighty says:

"Come back to your Lord, Well-pleased (yourself) and well-pleasing unto Him".

Monday, December 9, 2024

Rantsuwar da ake masu kaffara da Wanda ba'a masu kaffara

A cikin wannan jawabin Wanda babban limamin masallacin juma'a kasa dake Abuja farfesa Ibrahim Ahmad maqari yayi game da ire-iren rantsuwa inda ya bayyana cewa rantsuwa kala hudu ne.

Biyu daga cikin wadannan rantsuwan idan mutum yayi su sai yayi azumin kaffara guda uku yayin da sauran biyun bazai yi azumin kaffara ba.

Kala biyun da ake masu kaffara shine mutum ya rantse bazai yi Abu ba sai ya dawo yana so yayi ko Kuma ya rantse zaiyi abu ba sai ya dawo baiyi ba ya fasa, to wannan rantsuwan kala biyu ana masu kaffara.

Rantsuwan da ba'a masu kaffara sune mutum ya rantse baiyi abu ba sai daga baya ya baiyana yayi ko kuma mutum ya rantse yayi abu sai daga baya ya baiyana baiyi ba.

To wadannan rantsuwan ba'a masu kaffara ne idan mutum bisa rashin sani ne, Amma idan mutum da gangan yasan cewa abun da yayi da gaskene Kuma ya rantse baiyi ba to wannan ya wuce ayi kaffara sai dai neman tuba a wajen Allah Madaukakin sarki saboda wasa da mutum yayi da janibin mahalicci.

Allah (S.W.A) kare mana imaninmu.

Article Translation in English Language.

In this speech, the chief imam of the Friday Mosque in Abuja, Professor Ibrahim Ahmad Al-Maqari, spoke about the types of oaths, where he explained that there are four types of oaths. 

Two of these oaths, if a person takes them, then he fasts three times in expiation, while the other two do not fast in expiation. 

The two types of atonement are when a person swears that he will not do something and then comes back wanting to do it or he swears to do something and then returns and does not do it and breaks it, then these two types of oaths are called atonement. 

Oaths that are not expunged are the ones where a person swears not to do something and then confesses to it or a person swears to do something and then confesses and does not do it, then these oaths are not expiation only if a person does them Ignorance, but if a person deliberately swears that what he has done is true and he swears that he has not done it, then this is more than making atonement, but asking for repentance before God Almighty because of what a person has done with the Creator (The All mighty Allah). 

May Allah (S.W.A) protect our faith.