Wednesday, September 10, 2025

Menene hukuncin Zihari a Musulunci?

Menene hukuncin yin Zihari a Musulunci?

Menene Zihari?

Zihari shine miji ya kamanta ko ya sifanta matarshi da mahaifiyarshi da wata sifa na jikinsu ko suransu.

Zihari dabi'ace da ta samo asali a lokacin jahiliyan larabawa wadanda ke yi ga matayensu a duk lokacin da suke son rabuwa da su, sai su kamanta su da mahaifiyarsu ko yan uwansu na jini.

Shiyasa Allah madaukakin sarki ya saukar da aya a cikin Suratul Mujadala inda yayi hani da Kuma tabbatar da hukuncin kaffara ga duk musulmin da ya aikata irin wannan mummunar dabi'ar ta jahiliya.

Misalin Zihari shine miji yace wa matarshi "hancin ki irin na mahaifiyata ne" ko Kuma idanuwarki sak irin na mahaifiyata",

Saboda haka duk mijin da yace wa matarsa haka Ko makamancin haka, to yayi Zihari Kuma daga lokacin da ya furta hakan ga matarshi ta haramta a gareshi har sai yayi kaffara.


Yadda akeyin kaffara:

Kaffaran Wanda yayi  Zihari kalar kaffaran Wanda ya kashe rai bisa kuskure ne ko kuma yasha azumin Ramadan da gangan, shine 'yantar da bawa/baiwa ko Kuma Azumin wata biyu a jere wato kwanaki (60) ko Kuma ciyar da miskinai (60).

Allah madaukakin sarki ya kiyaye Mana harsunamu don matsayin Shugaban Halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam.




SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: