Thursday, December 12, 2024

Cikakken tarihin Annabi Muhammad

Cikakken tarihin Annabi Muhammad

Annabi Muhammad (S.A.W) an haife shi a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (AS) a Garin Makka ta Kasar Saudi Arabia, ya kuma yi wafati a ranar 8 ga watan Yuni shekaran 632 a birnin Madina na Kasar Saudi Arabia.

Shi ne ya kafa Musulunci, Addinin musulunci wanda ke da yawan mabiya biliyan 1.9 daga cikin Al'ummar Duniya biliyan 8 a halin yanzu.
Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance abun koyi ga dukkan musulmin duniya.
Mahaifinshi Abdullahi ya rasu tun kafin a haife Shi a lokacin mahaifiyasa Nana Aminatu (SAS) na dauke da cikinsa wata 6.

Bayan watanni uku da rasuwar Abdullahi Sai Nana Aminatu ta haifi Annabi Muhammad (S.A.W). Haihuwuwar ma'aiki (S.A.W) yazo da mu'ijizoji da abubuwan al'ajabi a wancan lokacin Kamar yadda yazo a tarihi, Alamonin bayyanarsa ya fara tun daga samun cikinsa har zuwa lokacin da yazo duniya inda Nana Aminatu (AS) ta ga Abubuwan Al'ajabin da bata saba gani ba.

Bayan haihuwar Annabi (S.A.W) mahaifiyarshi ta bayar da shi shayarwa ga Halimah bint Abi Dhuayb, saboda a wancan lokacin labarawa na bayar da jariransu shayarwa domin su samu nagartattun tarbiya da halaye.

Bayan ya shekara 6 a wajan sayyada Halima, nana aminitu ta karbo Shi domin takai ziyara wajen danginta garin Yasrib (Wanda yanzu ake Kira da Madina) inda suka tafi tare Annabi (S.A.W), suna Kan hanyarsu ta dawowa gida tare da baiwarta, Umm Ayman, Sai Nana Aminatu ta kamu da rashin lafiya inda ta rasu a kauyen Al-Abwa lokacin Annabi na da Shekaru 6 a duniya.

Bayan rasuwar mahaifiyarsa Aminatu (AS), ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) ya kasance cikakken Maraya Babu uwa Babu Uba a lokacin Yana da shekaru 6 kacal a duniya.
Bayan rasuwar Nana Aminatu (AS) ANNABI (S.A.W) ya koma karkashin kulawar baffansa wato dan uwan mahaifinsa, Abu Talib Inda ya rinka tafiya da shi kasuwanci da (fatauci) a wancan lokacin. 

Saboda rikon Amana da gaskiya yasa Mutane na matukar sha'awar yayi masu kasuwanci domin su bashi riba. 
Wanda hakan yasa daya daga cikin mata masu arzikin kasuwanci a wancan lokacin Nana Khadija (AS) ta bukaci baffansa Abu Talib da ya bata ANNABI (S.A.W) domin ya rinka mata kasuwanci, Kuma ya Aminta da wannan bukatuwar wacce ta zame mata sanadin habakar kasuwancinta Wanda bata taba gani ba a rayuwarta.

Hakika auren Nana Khadija da manzon Allah (S.A.W) ya kasance abun misali da kwaikwayo ga Al'ummar musulmi kasancewar Aure ne da ya ginu bisa soyayyar juna da tausayawa da girmama juna bisa tarin nagartattun halayen kowannensu.
Nana Khadija (RA) ta kasance mace ta farko da manzon Allah (S.A.W) ya fara so matsayin mata Kuma mace ta farko da ta bashi tarin gudunmawa da duka karfinta wajen ganin ya isar da sakon Allah madaukakin sarki.

A lokacin da manzon Allah (S.A.W) ya cika shekaru 40 a duniya, Allah madaukakin sarki ya bashi Annabta domin yayi kira izuwa kadaita Allah shi kadai a matsayin Abun bauta.
Kamar yadda ya kasance Al'ada ga sauran Annabawa da Allah ya aiko kafin zuwan manzon Allah (S.A.W) su kan fuskanci tsananin kiyayya da  kyama ga mutanen da aka aiko su, haka zalika Manzon Allah (S.A.W) ya fuskanci irin wannan kiyayya fiye ma da na sauran Annabawa.

Bayan saukar da wahayin farko ga manzon Allah (S.A.W) Wanda aka saukar mashi da Surah Iqra a lokacin da yake cikin kogon hira dake wajen garin Makkah.
Bayan dukkan alamu sun tabbatar da cewa manzon Allah (S.A.W) Annabin Allah ne, Nana Khadija ce farkon wacce ta fara mika wuya sannan sai Imam Ali Wanda yake yaro a lokacin bayan ya lura da manzon Allah (S.A.W) da Nana Khadija RA suna yin ibadah  tare ba irin ta bautar guma ka.

Kafin manzon Allah ya fara kiran sauran Al'umma zuwa ga Addinin musulunci sai da ya fara tara makusantarshi tukuna, wato kabilar Quraish, inda ya sanar da su cewa Allah ya aiko shi a matsayin Manzonsa ga Al'ummar duniya domin yayi masu bushara da sakon da Allah madaukakin sarki ya aiko shi na kadaitashi shi kadai a matsayin Abun bauta tare da amincewarsa a matsayin manzon Allah. 
Amma daga bisani suka ki karbar wannan Kiran manzon Allah (S.A.W) duk da cewa sun fi kowa sanin cewa babu wani mutum a garin Makkah mai irin nagartattun halayen manzon Allah (S.A.W).

Mutum na farko da ya karbi Addinin musulunci bayan Nana Khadija (R.A) da imam Ali (AS) Shine babban aminin Manzon Allah (S.A.W) , Sayyadina Abubakar (RA) Wanda ya samu labarin cewa abokinsa ya fara yin da'awar Annabta inda yake Kira da a zo a shiga wani sabon Addini, A lokacin Sayyadina Abubakar yayi tafiya, bayan ya dawo ne ya samu wannan labarin, Kuma bai jira ba inda yaje ya samu manzon Allah (S.A.W) game da labarin da ya fara ji a wajen Al'ummar gari, inda Manzon Allah (S.A.W) ya tabbatar masa da gaskiyar abun da ya ji Kuma nan take anan Sayyadina Abubakar (R.A) ya Mika wuya ba tare da sharadi ba.


Yawan 'ya'yayen manzon Allah (S.A.W). 
Manzon Allah (S.A.W) ya haifi 'yaya 7 ne a lokacin rayuwarsa kuma shida (6) daga cikinsu su Nana Khadija (RA) ce ta haife su. 
Qasim
Abdullah

Nana Fatima
Zainab
Ruqayya
Umm Kulthum.
Yayin da matar manzon Allah (S.A.W) sayyada Maria al-Qibtiyya (RA) ta haifi Ibrahim.



Article Translation in English Language.

Prophet Muhammad (S.A.W) was born in the year 570 after the birth of Prophet Jesus (AS) in Makkah, Saudi Arabia, and he died on June 8, 632 in Medina, Saudi Arabia. 

He is the founder of Islam, the religion of Islam, whose number is 1.9 billion of the world's 8 billion people at the moment. 

Prophet Muhammad (S.A.W) was a role model for all Muslims around the world. His father Abdullahi died before he was born when his mother Nana Aminatu was 6 months pregnant with him. 
Three months after the death of Abdullahi, Nana Aminatu gave birth to Prophet Muhammad (S.A.W), the birth of the servant (S.A.W) came with miracles and wonders at that time until the time He was born, Nana Aminatu saw wonders that she had not seen before. 
After the birth of the Prophet (S.A.W), his mother gave him breastfeeding to Halimah bint Abi Dhuayb, because at that time, Arabs gave their babies breastfeeding so that they would have good education and manners.

When He was 6 years old, Prophet's Mother, Nana Aminatu took Him from Halima to visit her family in the town of Yasrib (now Medina) where they went with the Prophet (S.A.W), on their way back home with her servant, Umm Ayman, then Nana Aminatu She fell ill and died in the village of Al-Abwa when the Prophet was 6 years old.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: