Yin addu'a bayan Kiran sallah sunnah ce mai karfi kamar yadda yazo a cikin hadisin da Jabir bin Abdullah (Allah ya yarda da shi ya ruwaito) Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi Yace: duk wanda ya karanta wannan Addu'ar
"Allahumma Rabba hadhihi-dda` watit-tammah, was-salatil qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wa b`ath-hu maqaman mahmudan-il-ladhi wa`adtahu" bayan ya saurari Kiran sallah to ceto na ya tabbata a gare shi ranar tashin kiyama.
Fassarar wannan Addu'ar shine:
"Ya Allah Ubangijin wannan cikakkiyar kira da tsayuwar Sallah, Ka yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) ceto da kuma falala, kuma ka daukaka shi zuwa ga matsayin da ka alkawarta masa".
Bayan an gama Addu'ar, ana kuma yin salati ga Annabi (S.A.W) da cewa
“Allahumma salli ala sayyidina Mohamad”.
Article Translation in English Language.
Praying after the call to prayer is a strong sunnah as mentioned in the hadith narrated by Jabir bin Abdullah (may God accept him) The Messenger of God, peace and blessings of God be upon him, said, “Whoever after listening to the Adhan says, ‘Allahumma Rabba hadhihi-dda` watit-tammah, was-salatil qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wa b`ath-hu maqaman mahmudan-il-ladhi wa`adtahu,’ then my intercession for him becomes binding on the day of resurrection.”
The translation of this dua is:
“O Allah, Lord of this perfect call and established prayer, grant Muhammad the intercession and favor, and raise him to the honored station You have promised him”.
After the adhan, it is also customary to send salutation upon the Prophet by saying “Allahumma salli ala sayyidina Mohamad”.
0 comments: