Ma'anar Istibra'i:
Istibra'i shine jira domin kubutar da mahaifa daga daukar ciki ko kuma zaman jiran a haife cikin da mace ke dauke dashi bayan tabbatar da samuwarsa.
Yadda ake yin istibra'i:
Yadda ake yin istibra'i shine idan matar da zatai istibra'i tana jinin haila to zata zauna har sai taga jini yazo mata sau uku.
Idan kuma bata ga jini ba saboda kuruciya ko yawan shekaru to zata zauna tsawon watanni uku.
Idan kuma tana da ciki ne to zata zauna har sai ta haifi abinda ke cikikinta.
Dalilan da suke sawa ayi istibra'i
1. Bauta.
Idan mutum yana da baiwa kuma ya kasance yana saduwa da ita sai ya sayar da ita ga wani mutum daban, to wanda ya saye ta bazai kusanceta ba har sai tayi istibra'i.
2. zina ko fyade
idan namiji ya sadu da mace bata hanyar aure ba, ta hanyar zina ne ko kuma fyade to wajibine tayi istibra'i kafin mijinta ya kusance ta in tana da aure ko kuma kafin tayi auren.
Allah a'alamu.

0 comments: