Wednesday, August 5, 2026

Sadakatu Jāriya a Musulunci.

Sadakatu Jāriya a Musulunci.

Sadakatu Jāriya a Musulunci ita ce sadaka da amfaninta ke ci gaba da gudana har bayan mutum ya rasu. Duk lokacin da mutane suke ci gaba da amfana da ita, mai yin sadakar yana ci gaba da samun lada.

Annabi Muhammad (SAW) ya ce:
"Idan ɗan Adam ya mutu, ayyukansa suna yankewa sai guda uku: sadaka mai gudana (Sadakatu Jāriya), 
Ilimi mai amfani 
ko ɗa na ƙwarai da yake yi masa addu'a."

 Misalan Sadakatu Jāriya sun haɗa da:

Gina masallaci.
Gina rijiyar ruwa ko samar da ruwan sha.
Gina makaranta ko ɗakin karatu.
Bayar da Alƙur'ani ko littattafan ilimi na addini.
Dasa itatuwan da mutane ko dabbobi za su ci amfaninsu.
Tallafa wa ɗaliban neman ilimi.
Gina asibiti ko cibiyar lafiya da jama'a ke amfani da ita.

Falalarta: 
Duk lokacin da wani ya ci gaba da amfana da wannan sadaka, mai yin ta yana ci gaba da samun lada daga Allah, ko da bayan rasuwarsa.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa mu kasance cikin masu yawaita Sadakatu Jāriya, Ya kuma karɓi ayyukanmu. Ameen.

0 Comment about the Post: