Friday, May 15, 2026

Falasdinawa na Gudanar da Zanga-zanga domin Cika Shekaru 78 da faruwan "Nakba", ranar da aka kafa ƙasar Israi'la.
Falasdinawa na Gudanar da Zanga-zanga domin Cika Shekaru 78 da faruwan "Nakba", ranar da aka kafa ƙasar Israi'la.

Miliyoyin Falasdinawa a Zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan da kuma al’ummomin ‘yan gudun hijira a duniya sun gudanar da bikin tunawa da cika shekara 78 da faruwar 'Nakba' a ranar 15 ga Mayu, inda suka sabunta kiran neman adalci da ‘yancin cin gashin kai da kuma ‘yancin komawa gidajensu na asali.

Kalmar “Nakba” na nufin “babbar masifa” a harshen Larabci, kuma tana nuni da tarwatsa Falasdinawa da aka yi a lokacin yakin 1948 da ya kai ga kafuwar kasar Isra’ila. Masana tarihi sun kiyasta cewa kusan Falasdinawa 750,000 ne aka tilasta musu barin gidajensu, yayin da daruruwan kauyuka da birane suka lalace ko aka kwashe su gaba daya.

Bikin na wannan shekara ya zo ne a lokacin da halin jin kai a Gaza ke da matukar tsanani, inda sama da mutane miliyan biyu suka rasa matsugunansu sakamakon yakin da ya yi ta gudana a watannin da suka gabata. 
Yawancin iyalai na ci gaba da rayuwa a cikin matsugunan wucin gadi da sansanonin ‘yan gudun hijira, musamman a kudancin Gaza.


A biranen Yammacin Kogin Jordan da suka hada da Ramallah da Hebron da Bethlehem, Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga, tarurrukan al’adu da jerin gwanon nuna hadin kai, suna dauke da tutocin Falasdinu da kuma makullan alama da ke wakiltar gidajen da suka rasa a 1948.

‘Yan gudun hijira da masu fafutuka suna cewa Nakba ba lamari guda daya ba ne na tarihi kawai, illa ci gaba da yanayin raba mutane da gidajensu. Yawancin iyalai na ci gaba da adana tsofaffin makullan gidaje da takardun filaye da sauran muhimman abubuwa da ke nuna alakar su da wuraren da suka fito.

Batun “‘yancin komawa gida” na daga cikin manyan muhimman matsalolin da har yanzu ba a warware ba a rikicin Falasdinawa da Isra’ila. Falasdinawa na cewa dokokin kasa da kasa, ciki har da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 194, na goyon bayan ‘yan gudun hijira su koma gidajensu.

Yayin da ake ci gaba da bikin a sassa daban-daban na duniya, Falasdinawa na cewa ranar Nakba ba kawai tunawa da abin da ya faru a baya ba ne, har ma da sabunta kiran neman ‘yanci da mutunci da hakkokin kasa.

Monday, November 3, 2025

Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100
Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100

Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100

Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin  Alƙur'ani cewa:

أَوْ كَالَّذِي مَرَّ عَلَى قَرْيَةٍ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَى عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّى يُحْيِ هَذِهِ اللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا فَأَمَاتَهُ اللَّهُ مِائَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالَ بَل لَبِثْتَ مِائَةَ عَامٍ فَانظُرْ إِلَى طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّةٌ وَأَنظُرْ إِلَى حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِلنَّاسِ وَأَنظُرْ إِلَى الْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِرُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ .

 Ma'ana:
    "Ko kuma kamar mutumin da ya wuce ta wata alkarya alhalin ta zama kango, sai ya ce: "Ta yaya Allah zai raya wannan bayan mutuwarta?"

Sai Allah Ya karbi rayuwarsa tsawon shekara ɗari, sannan Ya tashe shi, Ya ce: "Mene ne tsawon lokacin da ka zauna?" Sai ya ce: "Ai na zauna yini daya ne ko ma wani sashi na yinin." 

Sai Ya ce: "Ai ka zauna tsawon shekara dari ne, don haka dubi abincinka da abin shanka bai canja ba, kuma ka dubi jakinka mana ka gani, don Mu sanya ka ka zamanto aya ga mutane, kuma ka dubi kasusuwan ka gani yadda za Mu hada su, sannan Mu lullube su da nama."To lokacin da komai ya bayyana a gare shi, sai ya ce: "Na sani lalle Allah Mai iko ne a kan komai."

GA CIKAKKIYAR ƘISSAR:
Is'haq bin Bishr ya ce: Sa’id bin Bashir ya ba mu labari daga Qatadah, daga Ka’ab, haka nan Sa’id bin Abi ‘Arubah daga Qatadah, daga al-Hasan, haka nan kuma Muqatil da Juwaybir daga al-Dahhak, daga Ibn Abbas. 
Haka nan Abdullah bin Isma'il al-Suddi daga mahaifinsa, daga Mujahid, daga Ibn Abbas, da kuma Idris daga kakansa, Wahb bin Munabbih. Is'haq bin Bishr ya ce: “Dukkansu sun ba ni labari game da lamarin Uzair, kuma wasu sun ƙara bayani akan na wasu.”

Suka ce da isnadinsu:
Uzair bawan Allah ne salihi kuma mai hikima. 
Wata rana ya fita zuwa gonarsa don duba halin da ta ke ciki. 
Da yake dawowa, sai ya tsaya a wani wuri da ya ruguje. Wani babbar birni ne wanda aka samu wani azzalumin Sarki yakai musu hari, ya ruguza gari, ya kashe dukkan mutanen cikinsa. 
A daidai lokacin da Uzairu ya sauka wajen rana ta yi tsananin zafi. Ya shiga cikin wannan wuri yana kan jakinsa. 
Ya sauka daga jakin tare da wasu kwanduna biyu, ɗaya da ‘ya’yan itacen ɓaure ɗaya da inabi. Ya zauna a cikin inuwar wannan wuri, ya ɗauko  tasa, ya matse ‘ya’yan inabin da yake tare da shi a ciki. Sannan ya fitar da wata busasshiyar gurasa da yake tare da ita, ya jefa ta a cikin ruwan inabin domin ya jiƙa, ya kasance mai sauƙin ci. 
Bayan haka, ya kwanta a bayansa tare da jingina ƙafafunsa a bango.

Sai  ya dubi rufin waɗancan gidajen, ya ga sun tsaya, amma mutanen cikinsu sun hallaka. 
Ya kuma ga ƙasusuwan da suka zama tsofaffi su ka ruɓe. 
Sai ya ce: " Ko Ta yaya Allah zai raya waɗannan bayan mutuwarsu?" 

Ba shakka ya san cewa Allah madaukakin sarki na iya yin haka, amma ya faɗa ne cikin mamaki da tunani. 
Sai Allah ya aiko Mala’ikan Mutuwa ya karɓi ransa, kuma ya mutu har tsawon shekaru ɗari.

Bayan waɗannan shekaru ɗari, an samu abubuwa da dama a cikin al’ummar Banu Isra’ila. Allah ya aika wani mala’ika zuwa ga Uzair, ya fara sake halitta zuciyarsa don ya fahimci abubuwa, sannan idonsa don ya iya gani, domin ya ga yadda Allah ke raya matattu. Daga nan, mala’ikan ya gina jikinsa sannu a hankali yana kallo, sai aka rufe ƙasusuwansa da nama, da gashi, da fata. Sai mala’ikan ya hura masa rai, kuma duk wannan yana faruwa shi Uzairu yana gani da fahimta.

  Bayan ya farfaɗo, mala’ikan ya ce masa: "Kwana nawa ka yi a kwance?" Sai Uzair ya ce: "Na kwana rana guda ko rabin rana." Saboda ya farka lokacin yamma, kuma rana ba ta faɗi ba, sai ya ɗauka bai cika kwana ba. Mala’ikan ya ce: "A’a! Ka kwana shekaru ɗari!"

   Sai ya ce masa: "Ka duba abincinka da abin shanka." Ya duba, ya ga busasshen burodinsa da ruwan inabin a daidai yadda suka kasance, ba su canza ba. Allah ya kiyaye su daga lalacewa, kamar yadda ya ce: "Ba su canza ba."

  Sai mala’ikan ya tambaye shi: "Shin ka yi shakka?" Sai ya ce: "A’a, amma abin mamaki ne." Sai mala’ikan ya ce: "To, duba jakinka." Ya duba, ya ga ƙasusuwan jakinsa sun ruɓe sun zama ƙura. Sai mala’ikan ya kira waɗancan ƙasusuwan, suka tattaru suka haɗu, yana kallo. Sai ya sa musu jijiyoyi da tsokoki, ya rufe su da fata da gashi, sannan ya hura masa rai. Nan da nan jakin ya tashi yana haki yana duba sama, yana zaton tashin kiyama ne.

   Bayan haka, Uzair ya ce: "Na tabbatar Allah na iya yin komai!"

  Ya hau jakinsa ya koma garinsu. Amma sai ya taras mutanen garin ba su gane shi ba, shi ma bai gane su ba. Har ya isa gidansa, sai ya taras da wata tsohuwa makauniya, mai nakasa da shekarunta suka kai 120. Ita ce ‘yar aikinsu tun yana da shekaru 20. Sai ya ce mata:

"Ke kuwa, wannan gidan Uzair ne?"

Sai ta ce: "Eh, wannan gidan Uzair ne." Sai ta yi kuka ta ce: "Tun shekaru da yawa ba wanda ya ambaci Uzair, har an manta da shi."

   Sai ya ce: "Ni ne Uzair! Allah ya kashe ni na tsawon shekaru ɗari, sannan ya raya ni."

   Sai ta ce: "Subhanallah! Uzair yana daga cikin waɗanda Allah Ya ke amsa musu addu’a. Idan har kai ne Uzair, to ka roƙi Allah ya dawo min da idona don in gan ka, idan har kai ne zan gane ka."

   Sai ya yi addu’a, ya shafa hannunsa a idonta, nan da nan suka warke. Ya kama hannunta, ya ce: "Tashi da izinin Allah!" Sai Allah ya warkar da kafafunta, ta miƙe kamar wadda aka daure aka saki.

  Da ta ga shi, sai ta ce: "Na rantse, kai ne Uzair!"

    Sai ta fita ta sanar da mutanen Banu Isra’ila. A cikin su akwai ɗansa, wanda shekarunsa 118, da jikokinsa da suka girma. Sai mutanen suka zo suna kallonsa. Sai ɗansa ya ce: "Idan har kai ne babana, to yana da wata alama a bayansa."

   Sai suka duba bayansa, suka ga wannan alama, sai suka tabbatar da cewa shi ne Uzair. Sai Banu Isra’ila suka ce: "A baya, babu wanda ya haddace Attaura sai Uzair. Kuma Buktunassar ya ƙone Attaura, ba wanda ya haddace ta sai ‘yan kaɗan. To, sake rubuta mana ita!"

   Sai Uzair ya jagorance su zuwa inda mahaifinsa ya binne Attaura a zamanin Buktunassar. Suka tono ta, amma takardun sun ruɓe, rubutun ya ɓace. Sai Uzair ya zauna a ƙarƙashin wata itaciya, sannan Allah ya aika wasu haske guda biyu daga sama, suka shiga cikinsa. A nan ne ya tuna dukkan Attaura, ya sake rubuta ta ga Banu Isra’ila.

Saboda haka, Yahudawa suka ce: "Uzair ɗan Allah ne!" - (Sub'hanAllah!). Sun faɗi haka ne saboda wannan mu'ujiza ta sake dawo da Attaura da kuma irin matsayinsa a cikin su.

Wannan labari yana cikin abin da Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: "Muna so mu sanya ka a matsayin wata aya ga mutane." Uzair yana zaune tare da ‘ya’yansa masu tsufa, amma shi kansa matashi ne, domin an mayar da shi kamar lokacin da ya mutu yana da shekaru 40.

Abu Hatim al-Sijistani ya rera wata waka don bayyana mamakin wannan lamarin:

"Shugaban da ya tsufa, amma dansa da jikansa sun fi shi shekaru,
Yana ganin jikansa mai tafiya da sanda, amma shi kansa matashi ne.
Jikansa mai shekaru 90 yana tafiya cikin rauni,
Amma shi matashi ne mai ƙarfin jiki!"

Wannan ita ce mu’ujizar Annabi Uzair, wadda ta tabbatar da ikon Allah na raya matattu!

Wednesday, July 30, 2025

Tarihin fir'auna da Annabi Musa (AS)

 

Tarihin fir'auna da Annabi Musa (AS)

Fir'auna Sunan wani sarki ne da ya mulki bani israi'la bisa zulunci Wanda sai da Allah ya aiko masa da manzonsa Annabi Musa (AS) domin yayi mashi wa'azi da gargadi a bisa zulunci da kafircin da yake aikatawa a bayan kasa. Fir'auna ya rayu ne a kasar misra wato kasar Egypt.

Sunan fir'auna suna ne na sarauta da ake Kiran duk wani sarki da ya mulki kasar ta misra a wancan lokacin, saboda Sunan fir'auna na gaskiya shine Walid bn Musab.

Hakika duk musulmi yasan Sunan fir'auna domin sai da Allah madaukakin sarki ya ambace shi a cikin Alkur'ani sau 74 a wurere daban-daban.

Fir'auna ya kasance Azzalumin sarki Mai girman Kai da nuna dagawa Allah madaukakin sarki, baya ga Azabtar da kabilar bani israi'la da yayi na tsayon shekaru ya  Kuma karkashe masu 'ya'yayensu jarirai bisa zulunci da fargaban kada a haifi Annabi Musa (AS) Wanda bokayensa suka bashi labarin cewa shine zai kawo karshen mulkinsa a doron kasa.

Bayan sanun labarin cewa za'a haifi wani yaro Wanda shine zai kawo karshen mulkin zaluncinsa, Fir'auna yasa a rinka kashe duk wani yaro da aka haifa a misra, an ce sai da ya kashe jarirai sama da dubu Arba'in duk a kokarinsa na wanzuwar Annabi Musa (AS)......

A dan dakace mu Zamu cigaba.

Tuesday, December 24, 2024

Kasashe nawa ne a Duniya?

 Kasashe nawa ne a Duniya?

Akwai kasashe a duniya guda 195, wadanda suka fito daga nahiya 7 da muke da su a doron kasa, Afrika, Turai, Asiya, Amurka ta kudu, Amurka ta Arewa, Australia da Antarctica. 

Daga cikin Kasashen duniya 195 masu cikakken 'yanci da ake da su, 
Nahiyar Afrika ta kunshi kasashe 54, 
sai Nahiyar Asiya wacce ta kunshi kasashe 48, 
sai Nahiyar Turai mai kasashe 44, 
sai Amurka ta kudu ta kunshi kasashe 33, 
sai Amurka ta Arewa mai kasashe 2, sannan sai Australia ko (Oceania) mai kasashe 14.

Baya ga kasashe 195 da ake da su a duniya a kwai wasu sauran kananun kasashe ko tsibirai 55 da har yanzu Basu da cikakken 'yancin Cin gashin kansu, ma'ana kodai suna karkashin gudanarwar wasu Kasashen ne Ko kuma Suna gwagwarmayar samun 'yancin kai.

Article Translation in English Language.

There are 195 countries in the world, which come from the 7 continents that we have on earth, Africa, Europe, Asia, South America, North America, Australia and Antarctica. 

Among the 195 fully independent countries in the world, Africa consists of 54 countries, then the Asian continent which consists of 48 countries, then the European continent with 44 countries, South America consists of 33 countries, then North America with 2 countries, and then Australia or (Oceania) with 14 countries. 

In addition to the 195 countries that exist in the world, there are 55 other small countries or islands that still do not have full independence, meaning that they are either under the administration of other countries or are struggling for independence.


Sunday, December 15, 2024

Wace kasace Kasar Farisa?

 Wace kasace Kasar Farisa?


Kasar da ake kira da kasar Farisa itace kasar Iran Wanda cikakkiyar sunanta yanzu shine "Daular Musulunci ta Iran". 
Kasar Farisa wato Iran kasace mai dunbin tarihi wacce al'ummarta keda wayewa da Al'adu. 

Sunan Kasar ya samo asali ne daga sunan kabilar Farisa (Persia ko Pars) wadanda sune Al'umman mafi yawa a kasar. 

Article Translation in English Language.

The country called Persia is the country of Iran whose full name is now "Islamic Republic of Iran". 

The country of Persia that is Iran is a country with a long history whose people are civilized and cultured. 

The name of the country is derived from the name of the Persian tribe (Persia or Pars) who are the most numerous people in the country.

Saturday, December 14, 2024

Tarihin Prof Ibrahim Maqari

 Tarihin Prof Ibrahim Maqari

An haifi Sheikh Prof. Ibrahim Ahmad Maqari a ranar 15-09-1976 a birnin Zaria dake Jihar kaduna dake arewacin Najeriya. 

farfesa Ibrahim Maqari Malamin Addinin Musulunci ne kuma mai bin darikar tijjaniya.
masanin karabci ne Wanda a Kansa ne yayi karatunsa har zuwa matakin farfesa.

yayi karatunsa na firamari a birnin katsina a shekaran 1987 a lokacin mahaifinsa yana aikin malanta a Katsina Arabic college, bayan dawowar mahaifin nasa gida Zaria, farfesa Ibrahim Maqari yayi karatun sakandire a Jama'atu Arabic school dake Zaria kafin daga bisani ya tafi kasar Masar inda yayi digirinsa na farko a jimi'ar Al'azhar dake birnin alkahiran masar a shekaran 1999.

bayan ya dawo gida najeriya ya cigaba da karatunsa a jimi'ar Ahmadu Bello Zaria inda anan ma yayi digirinsa na biyu duk a fannin larabci a shekaran 2005 kafin daga bisani ya tafi jami'ar Bayero dake Kano inda yayi digirin digirgir wato PhD a turance a fannin larabci a shekaran 2009 tare da koyarwa kafin daga bisani ya zama farfesa a jami'ar ta Bayero.

Ya Fara koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello Zaria a shekaran 2009 kafin daga bisani ya koyar a jami'ar Jihar kaduna inda ya zama babban malami a shekaran 2010.

Farfesa Ibrahim Maqari ya koma jami'ar Bayero inda yayi karatun farfesa a fannin larabci da harsuna, ya kuma aje aikin koyarwa da Kansa a shekaran 2020.

Farfesa Ibrahim Maqari yayi karatun Addinin mai zurfi tun daga wajen mahaifansa da wasu manya-manyan Malamai a birnin Zaria kamar Malam tanimu kusfa da Malam Bala Kusfa. haka zalika farfesa Ibrahim Maqari ya haddace Alkur'ani mai girma tun yana dan shekara 14 a duniya a makarantar sheikh Yahuza zaria, ya kuma haddace manya-manyan Littafan hadisan Bukhari da Muslim.

Shine babban limamin masallacin juma'an kasa dake babban birnin tarayya Abuja inda yake gudanar da karatun Tafsir a lokacin watan Ramadan da sauran karatun fiqh.

Farfesa Ibrahim Maqari Yayi aure kuma Yana da 'Ya'ya inda ya aurar da daya daga cikinsu a shekaran 2024.


Article Translation in English Language.

Sheikh Prof. Ibrahim Ahmad Maqari on 15-09-1976 in Zaria city in Kaduna state in northern Nigeria. Professor Ibrahim Maqari is an Islamic teacher and a follower of the Tijjaniya sect. He is a classical scholar who has studied up to the level of a professor. 

He did his primary education in Katsina city in 1987 when his father was working as a scholar at Katsina Arabic college, after his father returned home to Zaria, Professor Ibrahim Maqari studied high school at Jama'atu Arabic school in Zaria before he went to Egypt where He obtained his first degree at Al'azhar University in the capital city of Egypt in 1999.


After he returned home to Nigeria, he continued his studies at Ahmadu Bello University, Zaria, where he completed his second degree in Arabic in 2005 before he went to Bayero University in Kano where he completed his PhD in English. 

In Arabic in 2009 and taught before becoming a professor at the University of Bayero. He started teaching at Ahmadu Bello University Zaria in 2009 before he later taught at Kaduna State University where he became a senior lecturer in 2010. 

Professor Ibrahim Maqari moved to Bayero University where he studied as a professor in the field of Arabic and languages, and went to work teaching with Kansa in 2020. 

Professor Ibrahim Maqari studied religion in depth from his parents with some great scholars in the city of Zaria such as Malam Tanimu Kusfa and Malam Bala Kusfa. 

In the same way, Professor Ibrahim Maqari memorized the Holy Qur'an when he was 14 years old in the school of Sheikh Yahuza Zaria, and he also memorized the great books of hadiths of Bukhari and Muslim. 

He is the chief imam of the National Mosque in the capital city of Nigeria, Abuja, where he conducts Tafsirul Qur'an during the month of Ramadan and other fiqh readings. Professor Ibrahim Maqari is married and has children where one  of them got married in the year 2024.
Tarihin Sheikh Dahiru Usman Bauchi (fitaccen Malamin Addinin Musulunci)
Tarihin Sheikh Dahiru Usman Bauchi (fitaccen Malamin Addinin Musulunci)

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar 29-Dhu al-Hijjah-1345 Wanda yayi daidai da 29 June 1927 miladiyan Annabi Isha (AS) a Garin Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya. 

Sheikh Dahiru Bauchi yayi karatun Alkur'ani a wajen mahaifinshi Alhaji Usman ya haddace Alkur'ani a wajensa kuma yayi sauran karatunsa a wajen wasu fitattun Malamai a lokacin kamar Sheikh Tijani Usman Zangon Bare-bari da Sheikh Abubakar Atiku da Sheikh Abdulqadir Zaria. 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yana da 'ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 ne da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin mai girma. 

daga cikin matayen da ya aura akwai 'yar shehunsa sheikh Ibrahim inyass haka zalika Sheikh Dahiru Usman Bauchi shine.  Mataimakin Shugaban Majalisar Kolin Malamai dake bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka kuma khalifan Sheikh Ibrahim inyass (Wanda shine khalifan Ahmadu Tijjani, Wanda ya kafa darikar tijjaniya).

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu a Ranar 27 ga watan nuwanban 2025 Yana da Shekaru 98 a lissafin Miladiya, yayin da ya shekara 101 a lissafin hijra.
Inda aka yi jana'izarshi a ranar Juma'a 28 ga watan nuwanban 2025.
Dubun-dubatan Al'ummar Musulmi daga sassa daban-daban na fadin Najeriya da ma ketare suka samu damar halartan jana'izarshi Wanda Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini ya Jagoranta kamar yadda marigayin ya bar wasiya


Article Translation in English Language.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi was born on 29-Dhu al-Hijjah-1345 which is equivalent to 29 June 1927 AD in Bauchi town located in northeastern Nigeria. 

Sheikh Dahiru Bauchi studied the Qur'an with his father Alhaji Usman and memorized the Qur'an with him and did his other studies with some prominent scholars at that time such as Sheikh Tijani Usman Zangon Bare-bari, Sheikh Abubakar Atiku and Sheikh Abdulqadir Zaria. 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi has 95 children, 406 grandchildren and 100 grandchildren. Out of this number, 77 of his children, 199 grandchildren and 12 grandchildren have memorized the Holy Quran. 

Among the wives he married there was the daughter of his sheikh, Sheikh Ibrahim inyass, as well as Sheikh Dahiru Usman Bauchi. 

The Vice President of the Supreme Council of Scholars that gives Islamic Fatawa in Nigeria and is a leading figure in the Tijjaniya sect in Nigeria and Africa and the caliph of Sheikh Ibrahim Inyass (who is the caliph of Ahmadu Tijjani, the founder of the Tijjaniya sect)

Thursday, December 5, 2024

Wace kasa tafi talauci a duniya?


Wace kasa tafi talauci a duniya?

Kasar da tafi kowace kasa talauci a duniya itace kasar Sudan ta kudu wacce ke nahiyar Africa, kasa ce wacce ta dogara da arzokin man fetur a matsayin hanyar samun kudin shiga. Amma rikicin kabilanci da na siyasa da kasar ke fama da shi ya jefa Al'ummar kasar cikin bakin talaucin da babu irinsa a duniya. 

Kamar yadda asusun bada lamani na duniya ya kiyassa tattalin arzikin Sudan ta kudu, GDP dinta shine Dalar Amurka billiyan $13.6B Wanda yasa take mataki na 157 a duniya. 
GDP ma'auni ne da ake amfani da shi wajen kimanta arzikin kasa ta yin amfani da abubuwan da ake samarwa a kasar domin amfanuwar 'yan kasar. 

Idan aka kwatanta GDP din kasar Sudan ta kudu da na Masar (Egypt) mai GDP Dalar Amurka tiriliyan $1.899t wacce itace tafi kowace kasa a nahiyar Afrika arziki ta dinka Sudan ta kudu sau 135.

Article Translation in English Language.

Which is the poorest Country in the world?
The poorest country in the world is South Sudan which is located in Africa, it is a country that depends on oil resources as a source of income. 

But the ethnic and political conflict that the country is suffering from has put the nation in the brink of poverty that is unprecedented in the world. 
According to the International Monetary Fund, South Sudan's economy is estimated to have a GDP of $13.6 billion, making it the 157th country in the world. 

GDP is a measure that is used to evaluate the country's wealth by using the things that are produced in the country for the benefit of the citizens. 
If you compare the GDP of South Sudan with that of Egypt (Egypt) with a GDP of USD 1.899 trillion which is 135 times more than any other country in Africa.

Tuesday, December 3, 2024

Prof Isa Ali Pantami biography

 Tarihin Prof Isa Ali Pantami

An haifi Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktobar 1972 a unguwar Pantami dake jihar Gombe a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Isa Pantami ya kasance ‘da ga Mallam Ali Ibrahim Pantami, mahaifiyarshi kuwa itace Malama Amina Umar Aliyu.

Ya fara karatun Al-Qur’ani a makarantar Allo kafin daga bisani ya shiga makarantar Firamare ta ‘Pantami Primary School’ inda a nan ne ya samu shaidar kammala karatun firamare, ya kammala karatun sakandire a makarantar Sakandire ta Kimiyya ta ‘Government Science Secondary School, Gombe.

Daga nan ne ya samu shigar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake jihar Bauchi, inda a nan ne ya samu damar kammala karatun Digiri a fannin Fasahar Kwafuta a shekarar 2003 tare da samun Digiri na 2 duk a fannin, a shekarar 2008. Pantami ya kammala karatun Digirin-digirgir a jami’ar Robert Gordon dake Aberdeen a kasar Sukotlan.

Ya fara aiki a jami’ar ATBU, inda yake koyar da ‘Information Technology’ kafin daga bisani ya koma Jami’ar Musulunci dake Madinah a matsayin shugaban Rubutun Fasaha a shekarar 2014.

A shekarar 2016, Pantami ya ajiye koyarwa, inda a nan ne shugaba Muhammad Buhari ya nada shi ya zama shugaban hukumar ‘NITDA’ a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.
Ya kasance babban malamin addinin Musulunci na sama da shekaru 20, ya kasance limamin sallah Juma’a a Najeriya da kasar Birtaniya.

Source: Jaridar Punch

Article Translation in English Language.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami was born on the 20th day of October 1972 in Pantami area in Gombe state in North Eastern Nigeria. 

Isa Pantami was born to Mallam Ali Ibrahim Pantami, and his mother was Mallama Amina Umar Aliyu. 

He started studying Al-Qur'an at Allo school before he joined Pantami Primary School where he got his primary school certificate and finished his secondary education at Government Science Secondary School. , Gombe. From there, he was admitted to Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) in Bauchi State, where he was able to complete his degree in Computer Technology in 2003 and obtained a 2nd Degree in the field in 2008. 

Pantami completed his PhD studies at Robert Gordon University in Aberdeen, Scotland. He started working at ATBU University, where he taught 'Information Technology' before he moved to the Islamic University in Madinah as the Head of Technical Writing in 2014. 

In 2016, Pantami retired from teaching, where President Muhammad Buhari appointed him to be the chairman of NITDA on September 26, 2016. 

He is a leading Islamic teacher for over 20 years, he was a Friday prayer leader in Nigeria and the UK. 

Source: Punch newspaper

Monday, December 2, 2024

Kasashen larabawa nawane a duniya?

 


Kasashen larabawa nawane a duniya?


jimillan Kasashen Laraba 22 ne a duniya wadanda suka fito daga nahiyar gabas ta tsakiya da kuma arewacin da gabas maso kuduncin nahiyar Afrika

Kamar dai yadda tarihi ya bayyana, Samun Kasashen larabawa a yankin nahiyar Afrika mai al'umma bakaken fata  ya samo asaline da mawaftakar yankin da gabas ta tsakiya, kasancewar tekun Bahar maliyane Kawai ya raba yankunan biyu.
Jerin Kasashen larabawa dake yankin gabas ta tsakiya.

Article Translation in English Language.

There are a total of 22 Arab countries in the world that come from the Middle East and the North and South East of Africa. 

As history revealed, the presence of the Arab countries in the African continent with black people has its origins in the region's proximity to the Middle East, as the Mediterranean Sea separates the two regions. 
Here are the List of Arab countries in the Middle East.

1- Bahrain
2- Iraq 
3- Jordan 
4- Kuwait
5- Lebanon
6- Oman
7- Palestine
8- Qatar
9- Saudi Arabia
10- Syria
11- Hadaddiyar daulan larabawa (UAE)
12- Yemen.

Jerin Kasashen larabawa dake yankin arewaci da gabas maso kuduncin afrika.

1- Algeria
2- Egypt
3- Somalia
4- Libya
5- Sudan
6- Tunisia
7- Mauritania
8- Morocco
9- Comoros Islands
10- Djibouti

Saturday, November 30, 2024

Yare nawane a Najeriya?


Yare nawane a Najeriya?

Kasar Najeriya na da yare sama da 371 wanda Kabila daban-daban ke amfani da su a matsayin harshensu don yin mu'amala a tsakaninsu amma Hausa,Yoruba da Igbo sune manya-manyan yarukan dake da kabilu Masu yawa a Kasar.

A alkalumar da shafin matambayi baya bata ya fitar Kashi 30 cikin dari na Al'ummar najeriya ke amfani da harshen Hausa, ma'ana yawan Masu amfani da harshen Hausa yakai miliyan 70 kenan na adadin miliyan 230,000,000 na yawan Al'umman najeriya wanda yawancinsu ke Arewacin najeriyan, yayin da sauran keda wannan kason.
Yoruba (15.5%), Igbo (15.2%), Fulani (6%), Ibibio (1.8%), Tiv (2.4%), Kanuri (2.4%), Ijaw (1.8%).

Article Translation in English Language.

The country of Nigeria has more than 371 languages ​​that are used by different tribes to communicate among themselves but Hausa, Yoruba and Igbo are the main languages ​​of many tribes in the country.

According to the statistics of the question page, 30 percent of the Nigerian people use the Hausa language, which means that the number of Hausa language users is 70 million out of the 230,000,000 million of the Nigerian population, most of whom are Northern Nigeria, while the rest are in this category. Yoruba (15.5%), Igbo (15.2%), Fulani (6%), Ibibio (1.8%), Tiv (2.4%), Kanuri (2.4%), Ijaw (1.8%).


Friday, November 29, 2024

Wanene shugaban kasar Najeriya na farko?



Shugaban Kasar Najeriya na farko shine Dakta Nnamdi Azikwe wanda ya hau karagar mulki a ranar 1 ga watan octoban 1960 ranar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawar mulkin mallaka, ana yi mashi lakabi da Zik.

Dan kabilar Igbo ne amma an haife shine a Arewacin Najeriya a jihar Neja inda daga baya ya koma birnin legas wajen kakanshi.

Article Translation in English Language.

The first president of Nigeria was Dr. Nnamdi Azikwe who took office on October 1, 1960, the day Nigeria gained independence from colonial rule, he was nicknamed Zik. 

He was a member of the Igbo tribe but was born in Northern Nigeria in Niger State where he later moved to the city of Lagos to his grandfather.


Thursday, November 28, 2024

tarihin kasar falasdinu


tarihin kasar falasdinu

Kasar falasdinu kasace dake yankin gabas ta tsakiya wacce Al'ummarta larabawa ne, kasa ce wacce ta kwashe shekaru a cikin rikici tsakaninta da israila, Kasar yahuda 'yan kama wuri zauna.


Kasar Falasdinu na da yawan Al'umma da yawansu yakai 5,483,450 Sanna a bangaren fadin kasa da yakai mu rabba'in kilomita 6,020Km².
tayi iyaka da Kasar Jordan ta bangaren gabas sannan ta yi iyaka da Kasar israila ta bangaren Kudu da yamma da arewa, Sai zirin Gaza wanda Ke tsakanin Israilan da Misra.

Yankin Kasar Falasdinu ya tsunduma cikin rikicin yaki ne tun daga shekaran 1967 lokacin da turawan yamma suka ba ragowar yahudawan da Hitler yayi ma Kisan gilla matsuguni a Kasar ta Falasdinu wacce yanzu Israilan ke mamayewa a kullum.

Article Translation in English Language.

Palestine is a country in the Middle East whose people are Arabs. It is a country that has been in conflict with Israel for years. 

The country of Palestine has a population of 5,483,450 and a land area of ​​6,020 km². It borders with Jordan on the east side and it borders with Israel on the south, west and north, except the Gaza Strip which is between Israel and Egypt. 

The Palestinian Territory has been involved in war since 1967 when the Westerners gave the remains of the Jews that Hitler massacred in the Palestinian Territory which is now occupied by Israel every day.

Wednesday, November 27, 2024

Wace kasa ce Kasar sham?

 


Kasar da ake Kira da Kasar Sham itace Kasar Syria wacce take nahiyar gabas ta tsakiya, ta yi iyaka da Kasar turkiya ta bangaren arewa Sai Kasar Lebanon ta bangaren yamma Sai Kasar Iraqi da Jordan ta bangaren Kudu.

Kasar Sham kasa ce mai dunbin tarihi a duniya wacce manya-manyan bayin Allah suka rayu a cikinta, duk da cewa Kasar Sham din da aka sani a shekaru masu yawa yanzu fadinta ya ragu sosai Sakamakon sauye-sauyen da aka rinka samu na mulki da yake-yake a tsakanin Daulolin Kasashen Larabawa.

Article Translation in English Language.

The country called Sham is the country of Syria which is located in the middle east continent, it borders with Turkey in the north and Lebanon in the west and Iraq and Jordan in the south. 

The country of Sham is a country with a long history in the world in which great servants of God lived, even though the country of Sham that was known for many years has now decreased greatly due to the changes that have been made in the government. - it is among the kingdoms of the Arab countries.

Friday, November 22, 2024

kasar da tafi yawan musulmai a duniya

 kasar da tafi yawan musulmai a duniya


Kasar da tafi yawan musulmi a duniya itace kasar Indonesia wacce keda yawan Al'ummar musulmai da yawansu yakai miliyan 242 (242,000,000).
Bayan Indonesia sai kasar Pakistan wacce keda yawan Al'ummar musulmai miliyan 240, (240,000,000), sai kasar India wacce ke mataki na uku da yawan Al'ummar musulmai 200, (200,000,000).
Ga sauran Kasashen da suke da yawan Al'ummar musulmai a duniya nan. 

Article Translation in English Language.

The country with the largest number of Muslims in the world is Indonesia, which has a population of 242 million Muslims (242,000,000). 
After Indonesia, there is Pakistan, which has a population of 240 million Muslims, (240,000,000), then India, which is the third country with a population of 200, (200,000,000). 
There are the list of other countries that have a large number of Muslim in the world.


1- Indonesia 242,000,000

2- Pakistan 240,000,000

3- India  200,000,000

4- Bangladesh 150,000,000

5- Nigeria 95,000,000

6- Egypt 85,000,000

7- Iran 82,000,000

8- Turkiye 72,000,000

9- Algeria 41,000,000

10- Sudan 39,000,000

Thursday, October 5, 2023

Yaki nawa Annabi Muhammad (S.A.W) yayi?

Yaki nawa Annabi Muhammad (S.A.W) ya halarta?

Bismillahir rahamanirrahim, 
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki tsira da amincinsa su kara tabbatuwa ga bawansa kuma manzonsa ANNABI Muhammadu (S.A.W).
A cikin wannan mukalan idan Allah ya nufa zamu gabatar maku da bayani game day Yakin da Manzon Allah (S.A.W) yayi a lokacin rayuwarsa.

Musulmai sun gwabza jumullar yakuna har guda ashirin da tara (29) a lokacin rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W), kuma Manzon Allah ya halarci tara (9) daga cikinsu yayin da sauran ya tura sahabbansa (Amincin Allah ya kara tabbata a gare su).

Yakokin da Manzon Allah (S.A.W) ya jagoranta Ko kuma ya halarta sune:

1-Badr, 
2-Uhud, 
3-Al-Khandaq, 
4-Quraydhah, 
5-Al-Mustaliqh, 
6-Khaybar, 
7-Al-Fath Makkah, 
8-Hunayn 
9-Ta'if


Article Translation in English Language.

Bismillahir Rahmanir Raheem, All praises and thanks be to Allah Almighty, may His peace and blessings be continue upon to his chosen servant and messenger PROPHET MUHAMMAD (S.A.W). In this article, if God wills, we will present you with the list of battles that the Messenger of God (S.A.W) participated during his lifetime. 

Muslims fought a total of twenty-nine (29) battles during the lifetime of the Prophet Muhammad (S.A.W), and the Messenger of God participated in only nine (9) of them while the rest he sent his companions (may God's peace be upon them). 
Here are The list of battles that the Messenger of God (S.A.W) led or participated in:

1-Battle of Badr, 
2-Battle of Uhud, 
3-Battle of Al-Khandaq, 
4-Battle of Quraydhah, 
5-Battle of Al-Mustaliqh, 
6-Battle of Khaybar, 
7-Battle of Al-Fath Makkah, 
8-Battle of Hunayn 
9- Battle of Ta'if

Tuesday, October 3, 2023

Tarihin Imam Malik ibn Anas (Ra)
Tarihin Imam Malik ibn Anas (Ra)

An haifi Imam Malik a garin Madinatul munawwwara garin da Manzon Allah (S.A.W) ya rayu a shekara ta 711CE zuwa shekarar 795 CE (miladiya) daidai da shekara ta 93 zuwa shekarar 179 (Hijra),
Lakabinsa shine Malik dan Anas dan Malik dan Abi Amir dan Amr dan Al-Haris dan Ghaiman dan khusain dan Amr dan Al-Haris Al-Asbahi amma Anfi sanin sa da Malik ibn Anas ko kuma imam malik da hausa da larabci (مالك بن أنس‎).

Imam malik Malamin Musulunci ne, Balarabe, kuma faqihi, Alkali ne, Malamin Tauhidi, da hadisi Malamin Sunnahr Manzon Allah tsira amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya rayu a garin madina inda ya karantar da bangarori daban-daban na Addinin musulunci.

Article Translation in English Language.

Imam Malik was born in the city of Madinatul Munawwwara, the city where the Messenger of God (S.A.W) lived in the year 711 CE to the year 795 CE (Miladiya) corresponding to the year 93 to the year 179 (Hijra). 

His title is Malik, son of Anas, son of Malik, son of Abi Amir, son of Amr, son of Al-Haris, son of Ghaiman, son of Khusain, son of Amr, son of Al-Haris Al-Asbahi, but he is better known as Malik ibn Anas or Imam Malik in Hausa and Arabic (مالك بن أنس‎ ). 

Imam Malik was an Islamic teacher, an Arab, and a jurist, a judge, a teacher of tawhid, and a hadith teacher of the Sunnah of the Messenger of God, 
may God's peace be upon him, he lived in the city of Medina where he taught various aspects of the Islamic religion.