Monday, November 3, 2025

Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100

Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100

Kissar Annabi Uzair Wanda Allah ya sake raya shi bayan ya mutu na tsawon shekaru 100

Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin  Alƙur'ani cewa:

أَوْ كَالَّذِي مَرَّ عَلَى قَرْيَةٍ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَى عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّى يُحْيِ هَذِهِ اللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا فَأَمَاتَهُ اللَّهُ مِائَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالَ بَل لَبِثْتَ مِائَةَ عَامٍ فَانظُرْ إِلَى طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّةٌ وَأَنظُرْ إِلَى حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِلنَّاسِ وَأَنظُرْ إِلَى الْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِرُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ .

 Ma'ana:
    "Ko kuma kamar mutumin da ya wuce ta wata alkarya alhalin ta zama kango, sai ya ce: "Ta yaya Allah zai raya wannan bayan mutuwarta?"

Sai Allah Ya karbi rayuwarsa tsawon shekara ɗari, sannan Ya tashe shi, Ya ce: "Mene ne tsawon lokacin da ka zauna?" Sai ya ce: "Ai na zauna yini daya ne ko ma wani sashi na yinin." 

Sai Ya ce: "Ai ka zauna tsawon shekara dari ne, don haka dubi abincinka da abin shanka bai canja ba, kuma ka dubi jakinka mana ka gani, don Mu sanya ka ka zamanto aya ga mutane, kuma ka dubi kasusuwan ka gani yadda za Mu hada su, sannan Mu lullube su da nama."To lokacin da komai ya bayyana a gare shi, sai ya ce: "Na sani lalle Allah Mai iko ne a kan komai."

GA CIKAKKIYAR ƘISSAR:
Is'haq bin Bishr ya ce: Sa’id bin Bashir ya ba mu labari daga Qatadah, daga Ka’ab, haka nan Sa’id bin Abi ‘Arubah daga Qatadah, daga al-Hasan, haka nan kuma Muqatil da Juwaybir daga al-Dahhak, daga Ibn Abbas. 
Haka nan Abdullah bin Isma'il al-Suddi daga mahaifinsa, daga Mujahid, daga Ibn Abbas, da kuma Idris daga kakansa, Wahb bin Munabbih. Is'haq bin Bishr ya ce: “Dukkansu sun ba ni labari game da lamarin Uzair, kuma wasu sun ƙara bayani akan na wasu.”

Suka ce da isnadinsu:
Uzair bawan Allah ne salihi kuma mai hikima. 
Wata rana ya fita zuwa gonarsa don duba halin da ta ke ciki. 
Da yake dawowa, sai ya tsaya a wani wuri da ya ruguje. Wani babbar birni ne wanda aka samu wani azzalumin Sarki yakai musu hari, ya ruguza gari, ya kashe dukkan mutanen cikinsa. 
A daidai lokacin da Uzairu ya sauka wajen rana ta yi tsananin zafi. Ya shiga cikin wannan wuri yana kan jakinsa. 
Ya sauka daga jakin tare da wasu kwanduna biyu, ɗaya da ‘ya’yan itacen ɓaure ɗaya da inabi. Ya zauna a cikin inuwar wannan wuri, ya ɗauko  tasa, ya matse ‘ya’yan inabin da yake tare da shi a ciki. Sannan ya fitar da wata busasshiyar gurasa da yake tare da ita, ya jefa ta a cikin ruwan inabin domin ya jiƙa, ya kasance mai sauƙin ci. 
Bayan haka, ya kwanta a bayansa tare da jingina ƙafafunsa a bango.

Sai  ya dubi rufin waɗancan gidajen, ya ga sun tsaya, amma mutanen cikinsu sun hallaka. 
Ya kuma ga ƙasusuwan da suka zama tsofaffi su ka ruɓe. 
Sai ya ce: " Ko Ta yaya Allah zai raya waɗannan bayan mutuwarsu?" 

Ba shakka ya san cewa Allah madaukakin sarki na iya yin haka, amma ya faɗa ne cikin mamaki da tunani. 
Sai Allah ya aiko Mala’ikan Mutuwa ya karɓi ransa, kuma ya mutu har tsawon shekaru ɗari.

Bayan waɗannan shekaru ɗari, an samu abubuwa da dama a cikin al’ummar Banu Isra’ila. Allah ya aika wani mala’ika zuwa ga Uzair, ya fara sake halitta zuciyarsa don ya fahimci abubuwa, sannan idonsa don ya iya gani, domin ya ga yadda Allah ke raya matattu. Daga nan, mala’ikan ya gina jikinsa sannu a hankali yana kallo, sai aka rufe ƙasusuwansa da nama, da gashi, da fata. Sai mala’ikan ya hura masa rai, kuma duk wannan yana faruwa shi Uzairu yana gani da fahimta.

  Bayan ya farfaɗo, mala’ikan ya ce masa: "Kwana nawa ka yi a kwance?" Sai Uzair ya ce: "Na kwana rana guda ko rabin rana." Saboda ya farka lokacin yamma, kuma rana ba ta faɗi ba, sai ya ɗauka bai cika kwana ba. Mala’ikan ya ce: "A’a! Ka kwana shekaru ɗari!"

   Sai ya ce masa: "Ka duba abincinka da abin shanka." Ya duba, ya ga busasshen burodinsa da ruwan inabin a daidai yadda suka kasance, ba su canza ba. Allah ya kiyaye su daga lalacewa, kamar yadda ya ce: "Ba su canza ba."

  Sai mala’ikan ya tambaye shi: "Shin ka yi shakka?" Sai ya ce: "A’a, amma abin mamaki ne." Sai mala’ikan ya ce: "To, duba jakinka." Ya duba, ya ga ƙasusuwan jakinsa sun ruɓe sun zama ƙura. Sai mala’ikan ya kira waɗancan ƙasusuwan, suka tattaru suka haɗu, yana kallo. Sai ya sa musu jijiyoyi da tsokoki, ya rufe su da fata da gashi, sannan ya hura masa rai. Nan da nan jakin ya tashi yana haki yana duba sama, yana zaton tashin kiyama ne.

   Bayan haka, Uzair ya ce: "Na tabbatar Allah na iya yin komai!"

  Ya hau jakinsa ya koma garinsu. Amma sai ya taras mutanen garin ba su gane shi ba, shi ma bai gane su ba. Har ya isa gidansa, sai ya taras da wata tsohuwa makauniya, mai nakasa da shekarunta suka kai 120. Ita ce ‘yar aikinsu tun yana da shekaru 20. Sai ya ce mata:

"Ke kuwa, wannan gidan Uzair ne?"

Sai ta ce: "Eh, wannan gidan Uzair ne." Sai ta yi kuka ta ce: "Tun shekaru da yawa ba wanda ya ambaci Uzair, har an manta da shi."

   Sai ya ce: "Ni ne Uzair! Allah ya kashe ni na tsawon shekaru ɗari, sannan ya raya ni."

   Sai ta ce: "Subhanallah! Uzair yana daga cikin waɗanda Allah Ya ke amsa musu addu’a. Idan har kai ne Uzair, to ka roƙi Allah ya dawo min da idona don in gan ka, idan har kai ne zan gane ka."

   Sai ya yi addu’a, ya shafa hannunsa a idonta, nan da nan suka warke. Ya kama hannunta, ya ce: "Tashi da izinin Allah!" Sai Allah ya warkar da kafafunta, ta miƙe kamar wadda aka daure aka saki.

  Da ta ga shi, sai ta ce: "Na rantse, kai ne Uzair!"

    Sai ta fita ta sanar da mutanen Banu Isra’ila. A cikin su akwai ɗansa, wanda shekarunsa 118, da jikokinsa da suka girma. Sai mutanen suka zo suna kallonsa. Sai ɗansa ya ce: "Idan har kai ne babana, to yana da wata alama a bayansa."

   Sai suka duba bayansa, suka ga wannan alama, sai suka tabbatar da cewa shi ne Uzair. Sai Banu Isra’ila suka ce: "A baya, babu wanda ya haddace Attaura sai Uzair. Kuma Buktunassar ya ƙone Attaura, ba wanda ya haddace ta sai ‘yan kaɗan. To, sake rubuta mana ita!"

   Sai Uzair ya jagorance su zuwa inda mahaifinsa ya binne Attaura a zamanin Buktunassar. Suka tono ta, amma takardun sun ruɓe, rubutun ya ɓace. Sai Uzair ya zauna a ƙarƙashin wata itaciya, sannan Allah ya aika wasu haske guda biyu daga sama, suka shiga cikinsa. A nan ne ya tuna dukkan Attaura, ya sake rubuta ta ga Banu Isra’ila.

Saboda haka, Yahudawa suka ce: "Uzair ɗan Allah ne!" - (Sub'hanAllah!). Sun faɗi haka ne saboda wannan mu'ujiza ta sake dawo da Attaura da kuma irin matsayinsa a cikin su.

Wannan labari yana cikin abin da Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: "Muna so mu sanya ka a matsayin wata aya ga mutane." Uzair yana zaune tare da ‘ya’yansa masu tsufa, amma shi kansa matashi ne, domin an mayar da shi kamar lokacin da ya mutu yana da shekaru 40.

Abu Hatim al-Sijistani ya rera wata waka don bayyana mamakin wannan lamarin:

"Shugaban da ya tsufa, amma dansa da jikansa sun fi shi shekaru,
Yana ganin jikansa mai tafiya da sanda, amma shi kansa matashi ne.
Jikansa mai shekaru 90 yana tafiya cikin rauni,
Amma shi matashi ne mai ƙarfin jiki!"

Wannan ita ce mu’ujizar Annabi Uzair, wadda ta tabbatar da ikon Allah na raya matattu!

0 Comment about the Post: