Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana'ar saukewa da tura fina-finai ta hanyar wayoyin salula a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin kare tarbiyyar al'umma da kuma inganta dabi'u da koyarwar addinin Musulunci.
A cewarsa, hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan samun korafe-korafe cewa wasu masu wannan sana'a na yada fina-finan batsa da sauran bidiyoyi da suka saba wa koyarwar Musulunci da al'adun Jihar Kano.
Ya ce an tura jami'an Hisbah domin sa ido da tabbatar da bin wannan umarni a fadin jihar, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu ya karya dokar zai fuskanci hukunci bisa tanadin dokokin Jihar Kano.
Dakta Aminuddeen ya kuma bukaci wadanda abin ya shafa su nemi wasu halaltattun hanyoyin samun abin dogaro, yana mai cewa manufar wannan mataki ita ce kare matasa daga abubuwan da ke lalata tarbiyya da kuma kiyaye kyawawan dabi'un al'umma.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano na ci gaba da aiwatar da dokokin da suka shafi Shari'a, tare da daukar matakai daban-daban domin kare tarbiyya da inganta dabi'un addinin Musulunci a jihar.

0 Comment about the Post: