Friday, June 19, 2026

Ministan harkokin wajen faransa ya bukaci Amurka ta matsa wa Isra’ila domin ta dakatar da kai hare-hare Lebanon.

Ministan harkokin wajen faransa ya bukaci Amurka ta matsa wa Isra’ila domin ta dakatar da kai hare-hare Lebanon.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya bukaci Isra’ila ta kawo karshen hare-haren soji da take kaiwa a Lebanon, sannan ya roki Amurka ta matsa wa Isra’ila lamba domin dakatar da rikicin.

A wata hira da gidan rediyon France Info ranar Juma’a, Barrot ya ce Faransa na ci gaba da kokarin shirya wani taron kasa da kasa domin neman tallafi ga sojojin Lebanon.

Wannan furucin ya zo ne bayan da Isra’ila ta ce ba ta kawar da yiwuwar kai hare-hare a wajen yankunan da sojojinta ke iko da su a kudancin Lebanon ba, duk da yarjejeniyar Amurka da Iran da ta bukaci a mutunta ikon mallakar Lebanon.

Halin da ake ciki a kan iyakar Lebanon da Isra’ila ya kara tsananta, bayan da Isra’ila ta sanar da mutuwar sojojinta hudu a Lebanon — lamarin farko tun bayan yarjejeniyar Amurka da Iran.

Faransa ta ce ana ci gaba da kokarin diflomasiyya domin hana rikicin kara yaduwa da kuma taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Lebanon.

0 Comment about the Post: