Aƙalla Falasɗinawa uku ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wani jirgin sama marar matuki na Isra’ila ya kai hari kan wata mota kusa da Masallacin Abu Khadra da ke yankin Rimal a yammacin birnin Gaza, kamar yadda majiyoyin lafiya suka bayyana.
Wakilin Al Jazeera a Gaza ya ce harin na ranar Alhamis shi ne fashewa ta farko da aka samu a yankin bayan wasu kwanaki na samun ɗan kwanciyar hankali.
Shaidun gani da ido sun ce motar da aka kai wa harin ta fararen hula ce. Daya daga cikin waɗanda aka kashe an bayyana shi da suna Abdul Jawad Abu Lebn, wanda ake shirin aurensa mako mai zuwa.
An gano katunan gayyatar aure a cikin motar.
Tun da farko a ranar Alhamis, an ce harin sojojin Isra’ila ya raunata wani masunci a gabar tekun Gaza da kuma wani mutum kusa da Khan Younis da ke kudancin Gaza. Haka kuma an ruwaito cewa an kashe wata yarinya a Beit Lahiya da ke arewacin Gaza.
Wadannan hare-hare sun faru ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta taimaka aka sanar a watan Oktoban bara. Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce sama da Falasɗinawa 1,000 ne aka kashe tun bayan fara tsagaita bude wutar, yayin da adadin wadanda suka mutu tun bayan fara yakin a watan Oktoban 2023 ya kai sama da 73,000.
A wani bangare kuma, Kwamitin Kula da Gudanar da Gaza ya ce ya kammala shirye-shiryen farfado da yankin da sake gina shi, kuma yana shirye ya fara aiki idan yanayi ya ba da dama.
Kwamitin ya ce tattaunawar da aka yi a Alkahira ta mayar da hankali kan sake gina ababen more rayuwa da tallafa wa bangaren lafiya da farfado da tattalin arzikin Gaza.
Sai dai ana ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar sake gina Gaza saboda ci gaba da fadada ikon sojin Isra’ila a wasu sassan yankin.
A Yammacin Kogin Jordan, kasashe takwas ciki har da Qatar da Saudiyya da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Indonesia da Pakistan da Masar da Turkiyya sun yi Allah wadai da abin da suka kira karuwar hare-haren wasu masu matsananciyar akidar Yahudawa kan Falasɗinawa, ciki har da kai hari kan masallatai kusa da Ramallah.
Hukumomin Falasɗinawa sun kuma ce an bayar da umarnin rusa wasu gidaje a yankin Hebron, yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali da fadada matsugunan Yahudawa.

0 Comment about the Post: