Wednesday, June 10, 2026

Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin Tekun Fasha.

Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin Tekun Fasha.

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) tare da Sojojin Iran sun sanar da kaddamar da wasu hare-haren soji da suka ce martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai a kudancin kasar.

A cikin sanarwar da aka fitar da safiyar Alhamis, Iran ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka kan wasu cibiyoyin sojin Amurka da ke kasashen Kuwait da Bahrain.

IRGC ta bayyana cewa rundunonin sararin samaniya da na ruwa sun kai hare-hare kan wasu muhimman wuraren sojin Amurka guda 18, ciki har da sansanonin Ali Al Salem da Ahmad Al Jaber a Kuwait, da kuma sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain. Iran ta ce an kai wadannan hare-hare ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da aka kai wa wuraren sojinta da wasu yankuna a kusa da Bandar Abbas.

A wata sanarwa dabam, Sojojin Iran sun ce sun kai hari ta amfani da jirage marasa matuka kan hedkwatar Rundunar Ruwa ta Biyar ta Amurka (US Fifth Fleet) da ke Bahrain. A cewar sanarwar, an kai hari kan na'urorin sadarwa da na'urorin hango makamai da kuma wasu sassan tsarin kariyar makamai masu linzami na Patriot.

Jami'an sojin Iran sun jaddada cewa rundunoninsu na cikin cikakken shiri domin ci gaba da daukar matakan martani idan bukatar hakan ta taso, suna masu cewa hare-haren za su ci gaba har sai an hukunta wadanda suka kai hare-haren farko.

Babban Hedkwatar Khatam al-Anbiya, wadda ita ce babbar cibiyar gudanar da ayyukan sojin Iran, ta bayyana cewa sabbin hare-haren sun tilasta dakatar da wani bangare na hare-haren da Amurka ke kai wa kasar. Hedkwatar ta yaba wa sojojin Iran bisa abin da ta kira martani mai karfi da tasiri.

A gefe guda, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran za su tsaya nan ba da jimawa ba, yana mai ikirarin cewa wasu manyan jami'an Iran sun tuntube shi domin neman dakatar da rikicin.

Sai dai IRGC ta musanta wannan ikirari, tana mai cewa ba gaskiya ba ne, kuma wani yunkuri ne na Amurka na kaucewa ci gaba da fuskantar yakin.

Wadannan abubuwa na faruwa ne bayan rahotannin wasu sabbin fashe-fashe da aka ji a lardin Hormozgan da sauran yankunan kudancin Iran, inda hukumomin kasar suka zargi Amurka da kai wasu sabbin hare-hare.

A wani mataki da zai iya kara tsananta rikicin, rundunar sojin Iran ta kuma sanar da rufe mashigin ruwa na Hormuz ga duk wani jirgin ruwa. Sanarwar ta ce daga yanzu ba za a bari jiragen dakon mai ko na kasuwanci su ratsa ta mashigin ba, tare da gargadin cewa duk wani jirgin da ya yi yunkurin wucewa zai iya fuskantar hari.

Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai a duniya, kuma duk wani cikas da ya samu na iya yin tasiri sosai ga kasuwannin makamashi da tsaron yankin da ma duniya baki daya.

Har zuwa yanzu dai, rikicin tsakanin Iran da Amurka na ci gaba da kara tsananta, yayin da bangarorin biyu ke musayar zarge-zarge da hare-haren soji. 

0 Comment about the Post: