Monday, August 3, 2026

Iran ta rataye mutum biyu bisa zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri.

Iran ta rataye mutum biyu bisa zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri.

Mahukuntan shari'a na Iran sun sanar da aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum biyu da aka samu da laifin yi wa Isra'ila leƙen asiri.

A cewar kafar yaɗa labarai ta bangaren shari'a ta Iran, Mizan, mutanen da aka kashe sun haɗa da Omid Behzad da Pouria Safvat. An ce kotu ta same su da laifin isar da bayanan sirri da suka shafi muhimman cibiyoyin soja da tsaro ga jami'an hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad.

Rahoton ya bayyana cewa mutanen sun taimaka wa hukumomin leƙen asirin Isra'ila wajen cimma manufofinsu ta hanyar samar da bayanan sirri kan cibiyoyin tsaro da na soja a lokacin rikicin da ake ci gaba da yi.

Sai dai mahukuntan Iran ba su bayyana lokacin da aka kama su ko kuma lokacin da aka gudanar da shari'arsu ba.

Tun bayan barkewar rikicin da ya shafi Iran, Isra'ila da Amurka a watan Fabrairu, Iran ta ƙara tsaurara matakan hukunta waɗanda ake zargi da leƙen asiri, inda aka samu ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama, ciki har da Amnesty International, sun ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar hukuncin kisa a Iran. Rahotanni sun nuna cewa an kashe akalla mutum 1,639 a ƙasar cikin shekarar da ta gabata, adadi mafi yawa tun shekarar 1989.

0 Comment about the Post: