Monday, August 3, 2026

Hanyoyin kula da Yaro a lokacin rarrafe.

Hanyoyin kula da Yaro a lokacin rarrafe.

Lokacin rarrafe wani muhimmin mataki ne a rayuwar yaro. A wannan lokaci, yaro yana fara amfani da hannuwa da gwiwowinsa wajen motsawa daga wuri zuwa wuri, yana taɓa abubuwa, yana ɗaukarsu, har ma yana kai su baki domin ya gane su. 
Wannan yana taimakawa wajen bunƙasa ƙwaƙwalwarsa da ƙarfin jikinsa da kuma koyon sabbin abubuwa. Duk da haka, wannan mataki na iya kasancewa mai haɗari idan ba a kula da shi yadda ya kamata ba.

Saboda haka, iyaye da masu kula da yara suna da muhimmiyar rawa wajen samar da muhalli mai tsafta da aminci da kuma dacewa da ci gaban yaro. 
Ya kamata su cire duk wani abu da zai iya jawo haɗari, su rufe wuraren da ke da haɗarin wutar lantarki, su hana yaro isa ga magunguna ko sinadarai masu cutarwa, sannan su riƙa sanya ido a kansa a kowane lokaci.

Haka kuma, yana da muhimmanci a ba yaro damar rarrafe cikin walwala a wuri mai aminci, domin hakan yana ƙarfafa tsokokinsa da ƙasusuwansa, da daidaiton motsinsa. A lokaci guda, a tabbatar yana samun abinci mai gina jiki da tsafta, da isasshen hutu domin jikinsa da kwakwalwarsa su ci gaba da bunƙasa yadda ya kamata.

Kulawa mai kyau a wannan mataki tana taimakawa wajen kare lafiyar yaro da haɓaka ci gabansa, da kuma shirya shi zuwa matakin tsayuwa da fara tafiya cikin ƙoshin lafiya.

Hanyoyi 10 da yakamata iyaye su kiyaye.

1. Tsabtace muhalli: A riƙa share ƙasa da tsaftace wurin da yaro ke rarrafe domin guje wa ƙwayoyin cuta.

2. Kare yaro daga haɗari: A cire abubuwa masu kaifi da ƙananan abubuwan da zai iya haɗiyewa da magunguna, da kayan wuta daga inda zai iya kaiwa.

3. Rufe matatun wutar lantarki: A yi amfani da murfin matatun wuta domin hana yaro saka yatsa ko wani abu a ciki.

4. Kula da matakala: A saka ƙofar kariya (safety gate) idan akwai matakala a gida.

5. Sanya tufafi masu dacewa: A sa masa tufafi masu sauƙi da ba za su hana motsinsa ba.

6. Kada a bar shi shi kaɗai: A riƙa sa ido a kansa yayin da yake rarrafe, musamman a wuraren da ke da haɗari.

7. Ba shi abinci mai gina jiki: Idan ya kai lokacin cin ƙarin abinci, a ba shi abinci mai kyau tare da ci gaba da shayar da shi nono.

8. Ƙarfafa motsa jiki: A ba shi damar rarrafe a wuri mai aminci domin ƙarfafa tsokoki da haɓaka ci gabansa.

9. Tsaftar hannu: A riƙa wanke hannunsa, musamman bayan ya gama rarrafe ko kafin cin abinci.

10. Duba lafiyarsa a asibiti: A tabbatar yana karɓar alluran rigakafi da kuma zuwa duba lafiyar yara bisa jadawalin asibiti.

Kulawa mai kyau a wannan mataki yana taimaka wa yaro ya girma cikin koshin lafiya, ya samu ƙarfin jiki, da kuma haɓaka ƙwarewar motsi da fahimtarsa.

0 Comment about the Post: