Shugaban Amurka, Donald Trump, da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da nufin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran da Fadar White House sun tabbatar da cewa an sanya hannu kan takardar ne ta hanyar intanet.
Jami’an Iran sun ce ƙungiyoyin tattaunawa daga ɓangarorin biyu za su gana a Geneva domin ci gaba da tattaunawa, amma ba za a yi wani babban bikin sanya hannu ba saboda an riga an kammala hakan ta yanar gizo.
Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “mai ƙarfi sosai”, yana cewa za ta hana Iran samun makaman nukiliya. Sai dai ya yi barazanar ɗaukar matakin soji idan Iran ba ta cika sharuɗɗan yarjejeniyar ba.
Yarjejeniyar ta ƙunshi shirin tattaunawa na kwanaki 60 kan shirin nukiliyar Iran da yiwuwar cire takunkuman da aka kakabawa ƙasar.
Jami’an Amurka sun ce shirin zuba jari na dala biliyan 300 ga Iran zai samu tallafi daga ƙasashen yankin, kuma za a yi amfani da kuɗin wajen sake gina muhimman abubuwan more rayuwa da suka lalace sakamakon yaƙin.
Iran ta ce an kammala shirin sake buɗe kadarorinta da aka kulle a ƙasashen waje tare da haɗin gwiwar babban bankin ƙasar.
Masana harkokin siyasa sun ce ɓangarorin biyu sun sha wahala sosai sakamakon yaƙin, inda Iran ta fuskanci matsalolin tattalin arziki da lalacewar gine-gine, yayin da Amurka ta fuskanci hauwawan farashin makamashi da asaran biliyoyin dala.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman batutuwan da suka shafi mashigin ruwan Hormuz da Lebanon.

0 Comment about the Post: