Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce nan ba da jimawa ba duniya za ta gane ko yarjejeniyar da aka shirya yi da Iran za ta tabbata ko a’a, yana mai nuna cewa har yanzu akwai yiwuwar yarjejeniyar ta rushe.
Da yake magana da manema labarai a taron G7 da aka gudanar a Faransa, Trump ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da ake sa ran za ta kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, wanda aka shirya yi ranar Juma’a, ba tabbas ba ne.
Trump ya yi gargadin cewa Amurka za ta iya komawa kai hare-hare kan Iran idan Iran ba ta “yi abin da ya dace ba”.
“Na yi tunanin za a kammala yarjejeniyar,” in ji Trump, amma ya ƙara da cewa wasu yarjejeniyoyi kan iya faduwa ko da ana ganin za su tabbata.
An ce yarjejeniyar da ake shirin yi tsakanin Amurka da Iran za ta kawo ƙarshen yaƙi a dukkan bangarori, ta kawo ƙarshen katangar sojan ruwa ta Amurka, sannan ta sake buɗe mashigin Hormuz, wanda yake da matuƙar muhimmanci wajen jigilar man fetur a duniya.
Jami’ai sun ce yarjejeniyar farko za ta buɗe hanyar tattaunawa na tsawon kwanaki 60 kan manyan batutuwa da suka haɗa da shirin nukiliyar Iran da tasirinta a yankin, da makomar mashigin Hormuz.
Jami’an Amurka sun ce an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar ta hanyar zamani, amma bangarorin biyu har yanzu suna da damar janyewa kafin rattaba hannu na ƙarshe.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar za ta haɗa da sassauta takunkuman da aka kakaba wa bangaren makamashin Iran da kuma tattaunawa kan ayyukan nukiliyar ƙasar.
Haka kuma akwai shirin sake gina tattalin arzikin Iran da aka kiyasta zai kai akalla dala biliyan 300, amma Trump ya ce hakan zai dogara ne kan matakin da Iran za ta ɗauka.
Sirrin da aka yi game da yarjejeniyar ya jawo suka daga wasu ‘yan majalisar Amurka, inda suke buƙatar a fitar da cikakken bayaninta ga jama’a.
Trump ya kuma yaba wa shugabannin Iran, inda ya bayyana su a matsayin “masu hankali”, sannan ya ce tattaunawar na iya haifar da sabuwar yarjejeniyar nukiliya da ta fi wadda aka cimma a shekarar 2015.
Ya kuma soki matakin soji na Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Lebanon, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga yarjejeniyar Amurka da Iran.

0 Comment about the Post: