Thursday, June 18, 2026

Matakai 14 dake cikin Yarjejeniyar da Amurka da Iran Suka cimma Domin kawo Ƙarshen Yaƙi a tsakaninsu

Matakai 14 dake cikin Yarjejeniyar da Amurka da Iran Suka cimma Domin kawo Ƙarshen Yaƙi a tsakaninsu

Amurka ta fitar da cikakken bayani kan yarjejeniyar fahimtar juna mai matakai 14 da ta cimma da Kasar Iran, wadda ke shirin kawo ƙarshen rikici tare da samar da hanyar cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.

Takardar mai suna “Memorandum of Understanding tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran” an bayyana ta ne bayan buƙatun jama’a na ganin cikakkun bayanan yarjejeniyar.

Ana sa ran za a sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Juma’a, sannan ƙasashen biyu za su shiga tattaunawa na tsawon kwanaki 60 domin kammala yarjejeniya ta ƙarshe.

Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz da warware matsalar tarin sinadarin nukiliyar Iran, da kuma samar da hanyar sassauta takunkuman tattalin arziki idan Iran ta cika alkawuran da aka amince da su.

Manyan abubuwan da ke cikin yarjejeniyar sun haɗa da:

Amurka da Iran sun amince da dakatar da hare-haren soji nan take a dukkanin fannonin rikicin, ciki har da Lebanon, tare da yin alkawarin ba za su kai wa juna hari ba.

Ƙasashen biyu sun amince su mutunta ikon juna da kuma guje wa tsoma baki cikin harkokin cikin gida.

Sun amince su kammala tattaunawar yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60.

Amurka za ta fara cire takunkumin ruwa da wasu matsalolin da aka sanya wa Iran, kuma ana sa ran kammala hakan cikin kwanaki 30.

Iran za ta taimaka wajen tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci a mashigar Hormuz da Tekun Farisa na tsawon kwanaki 60.

Amurka da ƙawayenta za su samar da shirin farfaɗo da tattalin arzikin Iran wanda zai kai dala biliyan 300.

Amurka ta amince ta fara shirin kawo ƙarshen takunkuman da aka sanya wa Iran bisa tsarin da za a amince da shi daga baya.

Iran ta sake tabbatar da cewa ba za ta kera makaman nukiliya ba, yayin da bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawa kan batun nukiliya.

Ƙasashen biyu sun amince su ci gaba da halin da ake ciki yanzu ba tare da ƙarin takunkumi ko tura ƙarin sojoji ba.

Amurka za ta bayar da izinin fitar da wasu kayayyakin man Iran da wasu mu’amalolin kasuwanci har sai an warware batun takunkumi.

Za a buɗe wasu kuɗaɗen Iran da aka kulle bisa tsarin da aka amince da shi.

Za a kafa wata hukuma ta sa ido domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar.

Idan aka kammala yarjejeniyar ƙarshe, ana sa ran za ta samu amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya ta hanyar ƙuduri mai ɗaurewa.

0 Comment about the Post: