Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri’ar neman kawo ƙarshen yaƙin da Amurka ke yi da Iran, bayan ta amince da wani kudurin dokar ikon yaƙi da zai takaita damar Shugaba Donald Trump na ci gaba da ayyukan soji ba tare da amincewar Majalisa ba.
Kudurin ya samu kuri’u 220 zuwa 204, inda dukkan ’yan Democrat da kuma ’yan Republican bakwai suka goyi bayansa. Uku daga cikin ’yan Republican da suka kada kuri’ar amincewa sun yi hakan ne a karon farko.
Dan Majalisar Wakilan Amurka daga Iowa, Zach Nunn, ya bayyana cewa ya goyi bayan kudurin ne saboda ci gaba da ayyukan soji na bukatar amincewar Majalisa.
Nunn ya ce: “Ba zan goyi bayan wani yaƙi mara iyaka ba.”
Sai dai kudurin na fuskantar cikas, domin makamantan kudurorin da aka gabatar a baya ba su kai ga teburin shugaban ƙasa ba. Idan kudurin ya isa wurin Trump, ana sa ran zai yi amfani da ikon veto wajen dakatar da shi.
Dan Republican Brian Mast, shugaban Kwamitin Harkokin Wajen Majalisar Wakilan Amurka, ya kare matakin gwamnatin Trump, yana mai cewa Iran na ci gaba da kasancewa barazana ga Amurka.
Kuri’ar ta zo ne yayin da ’yan majalisar ke shirin komawa jihohinsu domin yakin neman zaɓe gabanin zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na Amurka. Batun yaƙin Iran ya zama ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a yakin neman zaɓen.
Wani rahoto daga Congressional Budget Office (CBO) ya bayyana cewa yaƙin da aka shafe watanni shida ana yi ya janyo kashe kusan dala biliyan 38, kuma ana sa ran kuɗin yaƙin zai ƙaru da kusan dala biliyan 3 a kowane wata.
Rahoton ya kuma ce rikicin na iya ƙara hauhawar farashin kayayyaki a Amurka da maki 0.5 cikin 100 a cikin watanni uku na farko na shekarar 2027.
Wannan shi ne karo na uku da Majalisar Wakilan Amurka ta kada irin wannan kuri’a. A watan Yuni da Yuli ma ta amince da makamantan kudurori, yayin da Majalisar Dattawa ita ma ta yi ƙoƙarin takaita ikon gwamnatin wajen ci gaba da ayyukan soji.
A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Amurka, Majalisa ce ke da ikon ayyana yaƙi, yayin da shugaban ƙasa ke matsayin babban kwamandan sojoji. Dokar War Powers Act, wadda aka kafa bayan Yaƙin Vietnam, ta tanadi iyaka kan tsawaita ayyukan soji ba tare da amincewar Majalisa ba.

0 Comment about the Post: