Tuesday, August 25, 2026

Tinubu ya yi kira ga musulmi su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).

Tinubu ya yi kira ga musulmi su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin Eid-el-Maulud na bana, inda ya bukaci Musulmi da su yi koyi da kyawawan koyarwa da halayen Annabi Muhammad (SAW).

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Talata mai taken, “Eid-el-Maulud: Tinubu Ya Bukaci Musulmi Su Yi Koyi da Kyawawan Halayen Annabi Muhammad.”

Tinubu ya ce bikin Maulud bai kamata ya tsaya kawai ga tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ba, ya kamata Musulmi su yi amfani da lokacin wajen yin nazari kan rayuwarsu, addu’a da kuma koyon kyawawan halayen Manzon Allah.

Ya bukaci Musulmi su himmatu wajen bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman darussan ibada, juriya, haƙuri, tawali’u da sadaukar da kai.

Shugaban Ƙasar ya kuma yi kira ga malaman addinin Musulunci da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Najeriya addu’a tare da jan hankalin mabiyansu su aiwatar da darussan da suka koya daga rayuwar Annabi Muhammad (SAW) wajen nuna kishin ƙasa da biyayya.

Tinubu ya kuma roƙi Musulman da ke gudanar da bikin Maulud da su taimaka wa mabukata da marasa ƙarfi, domin nuna tausayi da haɗin kai a lokacin bikin.

Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya yi kira da a yawaita addu’o’i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar wasu sassan ƙasar.

0 Comment about the Post: