Monday, August 3, 2026

Ƙasar Iran Ta Musanta Gudanar da Tattaunawa da Amurka

Ƙasar Iran Ta Musanta Gudanar da Tattaunawa da Amurka

Ƙasar Iran ta bayyana cewa a halin yanzu ba ta gudanar da wata tattaunawa da Amurka, duk da rahotannin da ke nuna yiwuwar komawa teburin sulhu tsakanin kasashen biyu.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin kasar na tattaunawa da Oman ne kawai kan yiwuwar samar da wata hanyar wucewa ta wucin gadi a mashigin ruwa na Hormuz.

Sai dai ya jaddada cewa ko da an cimma matsaya da Oman, hakan kadai ba zai sa a sake bude mashigin ruwan ba, yana mai cewa halin da ake ciki ba zai sauya ba matukar abin da ya kira "ta'addancin Amurka" ya ci gaba.

Kalaman Baghaei na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da fuskantar tsamin dangantaka a Gabas ta Tsakiya bayan rikicin baya-bayan nan da ya shafi Iran da Amurka da Isra'ila.

Mashigin ruwan Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar danyen mai a duniya, lamarin da ke sa duk wani rikici a yankin ya kasance abin damuwa ga kasuwannin makamashi na duniya.

A lokaci guda, wannan matsayar ta Iran ta sha bamban da kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na cewa akwai yiwuwar gudanar da tattaunawa da Iran, abin da ke nuna cewa har yanzu akwai sabani mai zurfi tsakanin bangarorin biyu kan yiwuwar sake farfado da tattaunawar diflomasiyya.

0 Comment about the Post: