Sunday, July 12, 2026

Nehemiah Danjuma zuwa Bar, ya zama lauyan kurma na farko daga Arewacin Najeriya.

Nehemiah Danjuma zuwa Bar, ya zama lauyan kurma na farko daga Arewacin Najeriya.

Nehemiah Danjuma ya kafa tarihi bayan an kira shi zuwa Bar na Najeriya, inda ya zama lauya kurma na farko daga Arewacin Najeriya.

Danjuma, wanda ya fito daga karamar hukumar Jaba a jihar Kaduna, ya kammala karatun Digirin Lauya (LL.B) a Jami'ar Ilorin da sakamako mai aminci (Second Class Upper), kafin ya ci gaba zuwa Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law School), Abuja, inda ya kammala shirin Bar Part II.

Bayan an kira shi zuwa Bar, Danjuma ya bayyana farin cikinsa a shafinsa na X, inda ya rubuta: "Ni ne lauya kurma na farko daga Arewacin Najeriya. An kira ni zuwa Bar. Na kafa tarihi."

Nasararsa ta samu yabo daga abokai da abokan karatu da masu fafutukar kare haƙƙin masu nakasa, waɗanda suka bayyana cewa ya shawo kan ƙalubale da dama kafin cimma wannan matsayi.

Wani abokinsa a Makarantar Horar da Lauyoyi, Chukwu Nzubechukwu, ya bayyana cewa har ya koyi yaren alamar hannu (Sign Language) domin ya samu damar sadarwa da Danjuma cikin sauƙi, yana mai cewa Danjuma ya kasance abin koyi gare shi.

Danjuma ya kuma bayyana cewa a shekarar 2017 bai samu damar karantar Shari'a ba bayan da aka ba shi gurbin karatun Primary Education Studies a Jami'ar Ilorin. Sai dai ya ƙi karɓar gurbin, ya sake neman shiga jami'ar a shekarar 2018, inda daga bisani aka ba shi damar karantar Shari'a.

Baya ga karatu, Danjuma ya yi fice wajen fafutukar kare haƙƙin masu nakasa. A lokacin da yake Jami'ar Ilorin, ya wakilci ɗalibai masu nakasa a majalisar ɗalibai, sannan ya yi wa'adi biyu a matsayin Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Kurame ta Najeriya (NANDS), inda ya jagoranci shirye-shiryen da suka bunƙasa ayyukan ƙungiyar.

Haka kuma, tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024, ya kasance mai ba da shawara kan ci gaban matasa a Hukumar European Union Youth Sounding Board a Najeriya. Ya kuma samu horo na musamman kan dokokin kare haƙƙin masu nakasa a Loyola Law School da ke Los Angeles a ƙasar Amurka.

A lokacin da yake Makarantar Horar da Lauyoyi, Danjuma ya yi aikin horaswa a Babbar Kotun Tarayya ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma Ofishin Babban Lauyan Tarayya, inda ya samu ƙwarewa a binciken shari'a da rubuta takardun doka da kuma sa ido kan shari'o'i.

Bayan kammala karatunsa, Danjuma ya gode wa Voice of Disability Initiative (VDI) saboda tallafin da ta ba shi wajen biyan kuɗin mai fassara yaren alamar hannu, sannan ya yabawa JASAN Foundation bisa ba shi cikakken tallafin karatun makarantar koyon aikin lauya.

A halin yanzu, Danjuma na aiki a matsayin Jagoran Shirye-shirye a Voice of Disability Initiative, inda yake jagorantar ayyukan wayar da kai da bunƙasa shigar masu nakasa cikin al'umma.

Ana kallon wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga masu nakasa a Najeriya, tare da fatan za ta ƙarfafa gwiwar sauran matasa masu nakasa su cimma burinsu duk da ƙalubalen rayuwa.

0 Comment about the Post: