Wata kotu da ke gabashin ƙasar China ta yanke wa tsohon jami'in gwamnatin birnin Nanjing, Yang Youlin, hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin karɓar cin hanci da ya kai sama da yuan biliyan 2.2, kwatankwacin dala miliyan 325, cikin tsawon shekaru 30.
An kuma same shi da laifukan almundahanar kuɗin gwamnati da amfani da mukami ba bisa ƙa'ida ba, da kuma safarar kuɗaɗen haram. Kotun ta ce Yang ya yi amfani da mukamansa tsakanin shekarun 1993 zuwa 2023 wajen taimaka wa mutane samun kwangilolin gine-gine da canja wurin filaye da samun rance, a madadin karɓar kuɗi da kyaututtuka masu tsada.
Kotun da ke birnin Changzhou ta bayyana cewa laifukan nasa sun kasance masu matuƙar muni, tare da jawo babbar asara ga gwamnati da al'ummar ƙasar.
Shari'ar Yang na daga cikin yaƙin da Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, ke yi da cin hanci da rashawa, wanda ya shafi manyan jami'an gwamnati da sojoji da shugabannin ɓangaren bankuna.
Duk da cewa Yang ya amsa laifinsa tare da nuna nadama da kuma ba da haɗin kai ga masu bincike, kotun ta ce girman laifukan da ya aikata ya sa bai cancanci a sassauta masa hukuncin ba, don haka ta tabbatar da hukuncin kisa a kansa.

0 Comment about the Post: