Sunday, July 12, 2026

Kamfanin MTN Ya Ƙarfafa Matasa da Tallafin Miliyoyin Naira a Shirin Ƙirƙire-Ƙirƙire na jihar Kano.

Kamfanin MTN Ya Ƙarfafa Matasa da Tallafin Miliyoyin Naira a Shirin Ƙirƙire-Ƙirƙire na jihar Kano.

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya gudanar da shirin "100 Gathering" a jihar Kano domin ƙarfafa matasa ta hanyar bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci da haɗin gwiwa tsakanin masu basira.

Shirin ya haɗa matasa masu sana'o'i daban-daban da suka haɗa da 'yan kasuwa da masu fasaha da marubuta da masu ƙirƙirar abubuwan intanet da 'yan wasan bidiyo (gamers) da sauran masu ƙirƙire-ƙirƙire, inda suka samu damar musayar ra'ayoyi da nuna hazakarsu da kuma samar da hanyoyin magance matsalolin al'umma.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Manajan Tallace-tallace na MTN a yankin Arewa maso Gabas, Abu-Sufyan Aliyu, ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin haɗa matasa wuri guda tare da ƙarfafa su wajen samar da sababbin dabaru da za su kawo ci gaba ga al'umma.

Ya bayyana cewa an riga an gudanar da irin wannan shiri a Legas da Enugu da Aba kafin a kawo shi Kano, a matsayin wani ɓangare na ƙudirin MTN na tallafa wa matasan Najeriya a sassa daban-daban na ƙasar.

Aliyu ya ƙara da cewa an gudanar da gasar gabatar da dabarun kasuwanci (Pitch Competition), inda wanda ya zo na farko ya samu kyautar Naira miliyan 2.5, na biyu ya samu Naira miliyan 1.5, yayin da na uku ya samu Naira miliyan 1 domin tallafa musu wajen bunƙasa ayyukansu.

Shirin ya kuma ƙunshi gasan wasanni na bidiyo da baje kolin fasaha da zaman haɗa kai da kuma tattaunawar kasuwanci domin ƙarfafa kirkire-kirkire da kasuwanci tsakanin matasa.

Wadda ta lashe gasar, Samiat Yusuf, wacce ta kafa dandalin Applicant, ta ce manhajar na taimaka wa ƙungiyoyi wajen gudanar da aikace-aikace da zaɓen mahalarta da bibiyar halarta da sadarwa da kuma fitar da rahotanni cikin sauƙi.

Ta ce wannan tallafi zai taimaka musu wajen inganta manhajar, faɗaɗa ma'aikata da kuma kai ayyukansu ga ƙarin ƙungiyoyi.

MTN ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da shirin "100 Gathering" a wasu biranen Najeriya domin ƙarfafa matasa da haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa kasuwanci a faɗin ƙasar.

0 Comment about the Post: