Shugabannin Isra'ila sun bayyana jimaminsu kan rasuwar Sanatan Amurka, Lindsey Graham, inda suka bayyana shi a matsayin babban abokin ƙasar da kuma mai goyon bayan tsaron Isra'ila.
Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Graham ya yi imanin cewa tsaron Isra'ila da na Amurka abu ne da ba za a iya raba su ba. Ya ce rasuwar sanatan babbar rashi ce ga ƙasashen biyu.
Netanyahu ya ce, "Isra'ila ta rasa ɗaya daga cikin manyan abokanta, Amurka kuma ta rasa babban ɗan kishin ƙasa, ni kuma na rasa ƙaunataccen aboki."
Shugaban Isra'ila Isaac Herzog da Ministan Tsaro Israel Katz da Ministan Harkokin Waje Gideon Saar, da tsohon Firayim Minista Naftali Bennett su ma sun aike da saƙonnin ta'aziyyarsu.
Sun bayyana Graham a matsayin amini na gaskiya ga Isra'ila kuma ɗaya daga cikin fitattun masu goyon bayanta.
Marigayi Lindsey Graham ya shahara wajen nuna cikakken goyon baya ga alaƙar Amurka da Isra'ila tsawon shekarunsa a siyasa.
Rasuwarsa ta jawo alhini daga shugabanni a Amurka da Isra'ila, waɗanda suka yabawa jajircewarsa wajen kare tsaro da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

0 Comment about the Post: