Friday, July 17, 2026

Harin Isra'ila a Gaza ya kashe Falasɗinawa 14, ciki har da masu halartar jana'iza.

Harin Isra'ila a Gaza ya kashe Falasɗinawa 14, ciki har da masu halartar jana'iza.

Akalla Falasɗinawa 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Zirin Gaza a ranar Juma'a, ciki har da mutum takwas da ke halartar jana'izar wani da aka kashe a baya, kamar yadda jami'an lafiya da na kare fararen hula a Gaza suka bayyana.

Rahotanni sun ce jirgin yaƙin Isra'ila maras matuƙi ya kai harin ne kan masu zaman makoki da suka taru a wajen Masallacin Ahmad Yassin da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, yayin da suke shirin fara jana'izar. 
Harin ya kuma jikkata akalla mutane 20.

An kuma ba da rahoton wasu hare-hare a Beit Lahia, Az-Zawayda, Gaza City, Khan Younis da yankunan yammacin Nuseirat, inda wasu fararen hula, ciki har da mata, suka mutu ko suka jikkata.

Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai harin a tsakiyar Gaza, inda suka ce sun kai farmaki kan abin da suka bayyana a matsayin wata ƙungiyar mayaƙa. Sai dai sun ce suna duba rahotannin da ke cewa wasu fararen hula sun mutu ko sun jikkata.

Ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da harin, tana zargin Isra'ila da ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da kai hare-hare kan fararen hula.

Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki tun watan Oktoban bara, hare-hare na ci gaba da faruwa a Gaza. 
Masu sa ido kan rikice-rikice sun ce an samu ƙaruwa a hare-haren a watannin baya, lamarin da ke ƙara ta'azzara halin da fararen hula ke ciki.

0 Comment about the Post: