Monday, July 13, 2026

Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur'ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano.

Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur'ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano.

Fursunoni 61 da ke zaman hukunci a Gidan Gyaran Hali da ke Kurmawa a Jihar Kano sun kammala haddace Alƙur'ani Mai Tsarki a wani shirin gyaran hali da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta shirya.

Waɗanda suka kammala shirin sun haɗa da maza 55 da mata shida. Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce da dama daga cikinsu ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur'ani kafin su shiga gidan gyaran hali, amma ta hanyar horo da jajircewa da koyarwar addini, sun samu damar haddace Alƙur'ani gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa wannan nasara ta nuna irin tasirin shirye-shiryen gyaran hali na addini wajen sauya rayuwar fursunoni, tare da nuna ƙudirin hukumar na gyarawa da horarwa da sake dawo da su cikin al'umma kamar yadda Dokar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta shekarar 2019 ta tanada.

Domin karrama waɗanda suka kammala shirin, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya mai zaman kanta sun ba kowanne daga cikin waɗanda suka yi haddar kayan tallafi da suka haɗa da sabbin kaya da katifa da bargo da kuma tallafin kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa yayin komawarsu cikin al'umma.

Mai Kula da Gidajen Gyaran Hali na Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yaba wa Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagorancinsa wajen bunƙasa shirye-shiryen ilimi da sana'o'i da tarbiyya a gidajen gyaran hali a faɗin ƙasar.

Masanin ilimi, Farfesa Aliyu Harun, ya yabawa shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen mayar da fursunoni mutane nagari masu bin doka bayan sun samu 'yanci. 
Ita ma Shugabar Kwamitin Afuwar Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na inganta jin daɗin fursunoni, tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ci gaba da tallafa wa gidajen gyaran hali.

A yayin bikin yaye waɗanda suka kammala shirin, Limamin gidan gyaran hali, DSC Mohd Alkanawy, da Babban Limami, Imam Nasiru Abdu, sun bukaci waɗanda suka yi haddar su ci gaba da riƙe tarbiyya da kyawawan ɗabi'un da suka koya. Hakazalika, Hakimin Kawaji kuma Dan Ruwatan Kano, Alhaji Ibrahim Ado Bayero, ya mika takardun shaidar kammala shirin ga fursunoni 61.

0 Comment about the Post: