Gwamnatin ƙasar Belgium ta amince da haramta shigo da kayayyakin da ake samarwa a matsugunan Yahudawa da ke yankunan Falasɗinu da Isra'ila ta mamaye, lamarin da ya sa ƙasar ta shiga jerin ƙasashen Turai da ke ɗaukar irin wannan mataki.
An amince da matakin ne a taron majalisar ministocin gwamnati na ƙarshe kafin hutun bazara, domin cika alkawarin da gwamnati ta yi a shekarar da ta gabata sakamakon rikicin Gaza.
Ministan Harkokin Wajen Belgium, Maxime Prevot, ya bukaci Tarayyar Turai (EU) ta kafa dokar bai ɗaya da za ta hana shigo da kayayyakin da ake samarwa a waɗannan matsugunan.
Sai dai har yanzu ƙasashen EU ba su cimma matsaya guda ba kan batun.
Belgium ta bi sahun ƙasashe irin su Spain da Netherlands da Slovenia da Ireland, waɗanda suka ɗauki irin wannan mataki a cikin 'yan watannin nan.
Matakin ya biyo bayan rahotannin da ke zargin cewa wasu kayayyakin noma da aka samar a matsugunan Yahudawa ana sauya asalinsu tare da yi musu lakabi da cewa daga Isra'ila suke kafin a fitar da su zuwa kasuwannin Turai.
Tarayyar Turai ita ce babbar abokiyar kasuwancin Isra'ila, amma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan ko za a kafa dokar hana irin waɗannan kayayyaki a dukkan ƙasashen ƙungiyar.
Jami'an Belgium sun bayyana cewa manufar wannan mataki ita ce daidaita manufofin kasuwancin ƙasar da dokokin ƙasa da ƙasa da suka shafi matsugunan Isra'ila da ke yankunan Falasɗinu da aka mamaye.

0 Comment about the Post: