Saturday, July 18, 2026

Magajin Garin New York, Mamdani na Nazarin Yiwuwar Kama Netanyahu Idan Ya Ziyarci Birnin.

Magajin Garin New York, Mamdani na Nazarin Yiwuwar Kama Netanyahu Idan Ya Ziyarci Birnin.

Magajin Garin Birnin New York, Zohran Mamdani, ya bayyana cewa gwamnatinsa na tuntubar masana harkokin shari'a domin tantance ko akwai hurumin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, idan ya ziyarci birnin domin halartar taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da ake sa ran gudanarwa a watan Satumba.

A wata hira da jaridar The New York Times ta wallafa, Mamdani ya sake jaddada cewa yana ganin Netanyahu ya kamata ya fuskanci shari'a kan ayyukan da Isra'ila ta gudanar a Zirin Gaza. 
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar da sammacin kama Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama da zarge-zargen da Isra'ila ta musanta.

Mamdani, wanda ya yi alƙawarin neman a kama Netanyahu lokacin yakin neman zaɓensa, ya ce ofishinsa na duba irin ikon da doka ta bai wa birnin kan irin wannan mataki.

Ya ce, "Duk abin da doka ta ba mu damar yi a birnin New York, shi za mu yi, amma ba za mu ƙirƙiri sabuwar doka ba."

A martaninsa, Netanyahu ya soki Mamdani a wata hira da ya yi da wani mai gabatar da shirin rediyo a Amurka. 
Haka kuma, jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Danny Danon, ya ce Netanyahu zai halarci taron UNGA da za a yi a New York duk da kiraye-kirayen da ake yi na kama shi.

Matsayar Mamdani na nuna yadda ake samun sauyin ra'ayi a cikin Jam'iyyar Democrat game da goyon bayan Amurka ga Isra'ila. 
Binciken ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa adadin masu adawa da ci gaba da tallafin sojin Amurka ga Isra'ila na ƙaruwa a cikin jam'iyyar, yayin da wasu 'yan majalisa ma suka fara goyon bayan takaita irin wannan tallafi.

0 Comment about the Post: