An banka wa masallatai biyu wuta a yankin Yammacin Kogin Jordan wanda Isra'ila ke mamaye da shi, a wani hari da ake zargin wasu Yahudawa 'Yan kama wuri zauna ne suka kai.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a yankin.
Masallatan da ke kauyukan Qusra da Kour sun lalace matuka sakamakon gobarar. A masallacin Qusra, an kuma rubuta sakonnin ramuwar gayya a bango, ciki har da kalaman da ke nuni da wani sojan Isra'ila da aka kashe kwanan nan.
Wani mazaunin yankin mai suna Ahmed Abu Mahmoud ya ce ya ji motsi da misalin karfe 3:00 na dare, inda ya fito ya tarar da masallacin na ci da wuta.
Ya ce bai iya kashe gobarar shi kadai ba, sai ya nemi taimako.
A cewarsa, sojojin Isra'ila sun isa wurin amma daga bisani suka tafi.
Rahotanni sun ce hotunan kyamarorin tsaro daga kauyen Kour sun nuna wasu mutane uku sanye da kayan fararen hula suna tayar da wata fashewa a kofar masallacin kafin gobarar ta tashi.
Harin ya biyo bayan tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa hudu da kuma sojojin Isra'ila biyu a karshen mako.
Bayan haka, hukumomin Isra'ila sun kara yawan jami'an tsaro a yankin, sun rufe wasu manyan hanyoyi tare da kama sama da Falasdinawa 70 a wani mataki na dakile rikicin.
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa masallatan. Sai dai Falasdinawa da wasu 'yan adawar gwamnatin Isra'ila sun zargi gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu da yin sakaci wajen dakile hare-haren da Yahudawa 'yan kama wuri zauna ke kai wa Falasdinawa, suna gargadin cewa rikicin na iya kara bazuwa a yankin.

0 Comment about the Post: