Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce akalla Falasdinawa 16 ne suka mutu cikin awanni 48 da suka gabata, inda mutum bakwai suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai, yayin da aka ciro gawarwakin mutum tara daga karkashin baraguzan gine-ginen da suka rushe.
Ma'aikatar ta bayyana cewa asibitocin Gaza sun kuma karɓi mutum 16 da suka jikkata a wannan lokaci. Ta ƙara da cewa har yanzu ana kyautata zaton akwai wasu da ke makale ƙarƙashin baraguzai, amma jami'an ceto ba su iya isa gare su ba.
Wannan na faruwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'ila da Hamas suka cimma a watan Oktoban 2025.
Duk da cewa manyan faɗace-faɗace sun ragu, hukumomin lafiya na Gaza sun ce hare-haren sojojin Isra'ila a wasu sassan yankin sun ci gaba.
Ma'aikatar ta ce tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wutar, sama da mutum 1,000 ne suka mutu, yayin da fiye da 3,400 suka jikkata. Ta kuma bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a Gaza tun daga Oktoban 2023 ya haura 73,000, yayin da sama da mutum 173,000 suka jikkata.
A halin yanzu, tattaunawar ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar na ci gaba da fuskantar cikas, sakamakon rashin jituwa kan batun kwance damarar Hamas da kuma yadda sojojin Isra'ila za su janye daga Gaza.

0 Comment about the Post: