Saturday, July 4, 2026

Ƙasar Amurka ta gudanar da bukukuwan cika shekaru 250 da samun ‘yancin kai.

Ƙasar Amurka ta gudanar da bukukuwan cika shekaru 250 da samun ‘yancin kai.

Duk da tsananin zafin rana da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar, miliyoyin Amurkawa sun gudanar da bukukuwan cika shekaru 250 da samun ‘yancin kan Amurka, inda aka shirya fareti da kide-kide da baje kolin jiragen sama da kuma wasannin wuta a fadin kasar.

A birnin Washington DC, dubban mutane sun taru a National Mall da Lincoln Memorial da bakin kogin Potomac domin kallon wasan jiragen sama da sauran bukukuwan ranar.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jagoranci babban bikin tunawa da wannan rana a Mount Rushmore da ke jihar South Dakota. 
A jawabin da ya gabatar, ya yabawa al'ummomin da suka gina kasar tare da yin kira ga Amurkawa da su hada kai wajen ci gaba da gina makomar kasar.

A birnin New York kuwa, bukukuwan sun hada da jerin manyan jiragen ruwa na kasashe daban-daban tare da jiragen ruwan sojin Amurka da na Coast Guard da suka ratsa gabar New York Harbor kusa da mutum-mutumin Statue of Liberty.

Haka kuma, an gudanar da shahararren bikin wasan wuta na Macy's Fourth of July, inda aka harba kusan wasannin wuta 85,000 daga gadar Brooklyn da kogin East River da Hudson River tare da kade-kade da hasken laser.

Sauran manyan biranen da suka gudanar da bukukuwan sun hada da Chicago da Atlanta da Dallas, Denver da Los Angeles da San Francisco, inda aka shirya bukukuwan al'umma da wasannin nishadi da shirye-shiryen iyalai domin murnar wannan gagarumin tarihi.

0 Comment about the Post: