Wani bene mai hawa uku ya rushe a yankin Alakija da ke Jihar Legas, inda ake fargabar mutane da dama sun makale a ƙarƙashin Baraguzan ginin.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis da misalin ƙarfe 11:40. Har zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka makale a cikin ginin ba.
Mazauna yankin da masu wucewa sun taru a wajen da ginin ya rushe suna jiran isowar jami’an agajin gaggawa da masu ceto.
Hukumomi ba su bayyana musabbabin rushewar ginin ba, haka kuma ba a tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni ba.
Ana sa ran fara aikin ceto yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano mutanen da ke ƙarƙashin tarkacen ginin.

0 Comment about the Post: