Hare-haren sojin Isra’ila sun kashe aƙalla Falasɗinawa hudu, ciki har da wata yarinya mai shekaru 13, tare da jikkata wasu da dama a Zirin Gaza, yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da kuma gudanar da farmaki a ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, Wafa, ya ruwaito cewa wani jirgin sama mara matuki na Isra’ila ya kai hari a yankin al-Salatin, yammacin Beit Lahiya a arewacin Gaza, inda mutane biyu suka mutu wasu kuma suka jikkata.
A kudancin Gaza, musamman Khan Younis, an ce sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata tanti da take ɗauke da Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu. Harin makami mai linzami ya jikkata mutane da dama, yayin da asibitin Nasser ya tabbatar da mutuwar wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.
Haka kuma, wata yarinya mai shekaru 13 mai suna Eileen al-Farra ta mutu sakamakon raunukan da ta samu daga gutsuren harsashin tankin yaƙi a kudancin Gaza.
Kwamitin Kasa da Kasa na Red Cross (ICRC) ya bayyana cewa ya taimaka wajen mayar da Falasɗinawa 14 da Isra’ila ta saki daga tsare zuwa Asibitin Al-Aqsa Martyrs, inda suka sake haɗuwa da iyalansu.
Kungiyar ta ce ta taimaka wajen mika sama da mutum 2,500 da aka saki daga tsare tun shekarar 2023, amma ta ƙara da cewa Isra’ila ba ta ba ta damar ziyartar Falasɗinawan da ake tsare da su a gidajen yari tun watan Oktoban 2023 ba.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce yaƙin da ake ci gaba da yi ya yi sanadin mutuwar fiye da Falasɗinawa 73,000 tare da jikkata sama da 173,000 tun Oktoban 2023.
A yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, an ruwaito cewa wasu ‘yan kama wuri da Isra’ila ke mara wa baya sun shiga harabar Masallacin Al-Aqsa tare da kariyar ‘yan sanda.
Hukumomin Falasɗinu sun zargi Isra’ila da takaita zirga-zirgar masu ibada tare da hana wasu shiga masallacin.
A Hebron kuma, an ce sojojin Isra’ila sun hana kiran salla a Masallacin Ibrahimi har tsawon kwanaki takwas a jere.
Sojojin Isra’ila sun kuma gudanar da samame a wasu yankuna na Yammacin Kogin Jordan, inda suka kama Falasɗinawa tare da jikkata wani mutum yayin wani samame kusa da Kudus.
Kungiyoyin Falasɗinu sun yi kira ga ƙasashen duniya su matsa lamba kan Isra’ila dangane da abin da suka kira ƙara kai hare-hare kan ma’aikatan lafiya, kungiyoyin farar hula da kuma fursunoni.

0 Comment about the Post: