Friday, June 19, 2026

Majalisar dinkin duniya ta ce a kowace rana sai Isra’ila ta kashe aƙalla yaro daya a Gaza tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Octoba.

Majalisar dinkin duniya ta ce a kowace rana sai Isra’ila ta kashe aƙalla yaro daya a Gaza tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Octoba.

Kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da yara (UNICEF) ya ce ana kashe aƙalla yaro ɗaya a kowace rana a Gaza tun bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Octoban bara 2025.

Mai magana da yawun UNICEF, James Elder, ya bayyana tsagaita bude wutar da cewa “yaudara ce mai muni da ke jawo asarar rayuka,” yana mai cewa hare-hare na ci gaba da hana tsagaita bude wutar kare rayukan yara.

A cewar UNICEF, sojojin Isra’ila sun kashe akalla yara Falasɗinawa 265 tun watan Oktoban 2025, yayin da fiye da 400 suka jikkata, da dama daga cikinsu na fama da munanan raunuka.

Elder ya ce an kashe yara a gidaje da makarantu da wuraren taruwar jama’a, ciki har da lokacin da suke buga ƙwallo ko kamun kifi.

Ya ambaci wasu al’amura na baya-bayan nan, ciki har da wani yaro mai shekaru 2 da aka harbe ya mutu, wani yaro mai shekaru 13 da aka kashe a cikin tanti, da kuma wani yaro mai shekaru 5 da mahaifinsa da suka mutu sakamakon wani hari ta sama.

UNICEF ta yi gargadin cewa yara da dama da suka ji rauni na buƙatar fitar da su zuwa wasu wurare domin samun magani, yayin da takaita shigar magunguna da kayan agaji ke ƙara haɗarin kamuwa da cututtuka.

Elder ya ce tsoro da rashin galihu da tashin hankali sun zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum ga yaran Gaza.

Hukumomin lafiya na Falasɗinu sun ce hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga Oktoban 2023 sun kashe sama da Falasɗinawa 73,000 tare da jikkata fiye da 173,000, bisa alkaluman da rahoton ya ambata.

UNICEF ta kuma ce daruruwan yara sun mutu ko sun jikkata a Lebanon sakamakon ƙarin tashin hankali a yankin.

0 Comment about the Post: