Friday, June 19, 2026

Amurka Ta Shirya Sabuwar Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Tsakanin Isra’ila da Lebanon a Mako Mai Zuwa

Amurka Ta Shirya Sabuwar Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Tsakanin Isra’ila da Lebanon a Mako Mai Zuwa

Amurka ta sanar da cewa za a gudanar da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Isra’ila da Lebanon a birnin Washington DC mako mai zuwa, yayin da ake kokarin tabbatar da tsagaita bude wuta da cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana hakan ne jim kadan bayan Isra’ila da Hezbollah sun sanar da sabon tsagaita bude wuta a Lebanon, bayan sabon rikici da ya yi barazanar kawo cikas ga yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen yakin.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya tattauna da Shugaban Lebanon Joseph Aoun a ranar Juma’a, inda ya ce tattaunawar kai tsaye tsakanin Lebanon da Isra’ila ita ce hanya mafi dacewa don sake gina kasar da farfado da tattalin arziki da kawo karshen yawan rikice-rikice.

An tsara tattaunawar ne a ranakun 23 da 25 ga Yuni, inda gwamnatocin kasashen biyu za su tattauna hanyoyin samun zaman lafiya na dindindin.

Isra’ila da Lebanon sun fara tattaunawa kai tsaye a watan Afrilu, karo na farko tun shekarar 1993. Bayan haka sun sake gudanar da wasu tattaunawan a watan Yuni, wanda ya kai ga dakatar da fada na wani lokaci.

Sai dai Hezbollah ba ta cikin tattaunawar, lamarin da ya sa samun ci gaba ya yi wahala. Kungiyar da Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare, inda hare-haren Isra’ila suka kashe akalla mutane 47 a kudancin Lebanon a tsakar daren ranar Juma'a.

Gwamnatin Lebanon ta kuma bukaci Isra’ila ta janye daga kudancin kasar, yayin da take aiki kan shirin da Amurka ke goyon baya na rage karfin makamai na Hezbollah.

Ci gaba da fada ya kawo cikas ga yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya zargi Isra’ila da neman “yakin da ba zai kare ba.”

0 Comment about the Post: