Friday, June 26, 2026

Kotu Ta Yankewa Dan Boko Haram Hukuncin Kisa Kan Hare-haren Maiduguri Na shekaran 2015.

Kotu Ta Yankewa Dan Boko Haram Hukuncin Kisa Kan Hare-haren Maiduguri Na shekaran 2015.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yankewa wani dan kungiyar Boko Haram, Alkali Yarima wanda aka fi sani da La’ari, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin shiga hare-haren ta’addanci da aka kai a Maiduguri a shekarar 2015.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, inda ya ce an samu Yarima da laifin shiga ayyukan ta’addanci da suka shafi hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka.

Kotun ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na rai-da-rai kan laifin samun horon amfani da makamai da kuma shirya aikata ta’addanci.

Bugu da ƙari, kotun ta ba shi shekaru 35 a gidan yari kan wani laifi, da kuma shekaru 30 kan wani laifin daban. Haka kuma an ƙara masa wasu hukuncin shekaru 10 kan wasu tuhume-tuhume.

Gwamnatin Tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda bakwai na ta’addanci a kansa, inda ta zarge shi da kasancewa ɗan kungiyar Boko Haram wadda aka haramta a Najeriya, tsakanin shekarun 2009 zuwa 2015.

Masu gabatar da ƙara sun ce Yarima ya karɓi koyarwar Boko Haram daga wanda ya kafa ƙungiyar, Mohammed Yusuf, sannan ya shiga wasu ayyukan da suka shafi ta’addanci.

Kotun ta kuma ji cewa ya taɓa zuwa wata ƙasar Larabawa domin samun horon amfani da makamai da dabarun yaƙi.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wannan hukunci na nuna ƙudurin gwamnati na yaƙi da ta’addanci da sauran laifukan da suka shafi tsaro a Najeriya.

An sauya wurin gudanar da shari’ar daga Kainji da ke Jihar Neja zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

0 Comment about the Post: