Monday, June 22, 2026

Jarumin Fim ɗin Breaking Bad, Giancarlo Esposito, Ya Rungumi Addinin Musulunci A ƙasar Saudi Arabia.

Jarumin Fim ɗin Breaking Bad, Giancarlo Esposito, Ya Rungumi Addinin Musulunci A ƙasar Saudi Arabia.

Rahotanni sun bayyana cewa shahararren ɗan wasan kwaikwayo na Amurka, Giancarlo Esposito, wanda ya yi fice a cikin shirin fim ɗin Breaking Bad, ya karɓi addinin Musulunci a yayin ziyararsa zuwa Saudi Arabia.

Wani bidiyo da Turki Al-Sheikh, shugaban Hukumar Kula da Nishaɗi ta Saudi Arabia, ya wallafa ya nuna Esposito yana sallah a wani masallaci tare da wasu daga cikin ma’aikatan shirya fim ɗin Seven Dogs.

Esposito

Al-Sheikh ya ce hulɗar Esposito da Musulmai da kuma abubuwan da ya gani yayin aikinsa a yankin sun taimaka masa wajen fahimtar addinin Musulunci. Ya ƙara da cewa jarumin ya karanta kalmar shahada tare da shiga sallah.

Sai dai ba a tabbatar da ainihin wurin da aka yi sallar ba, domin wasu rahotanni da masu amfani da kafafen sada zumunta sun ce wataƙila an dauki bidiyon a Masallacin Hassan II da ke Morocco ba Saudi Arabia ba.

A wani tsohon hira da aka yi da shi, Esposito ya bayyana yadda ziyararsa zuwa Morocco ta shafe shi, inda ya yaba da yadda al’umma ke nuna ibada da tsantsar imani.

Rahoton ya fito ne bayan Esposito ya halarci bikin nuna fim ɗin Seven Dogs a Casablanca tare da wasu jarumai da daraktoci.

Giancarlo Esposito ya shahara a duniya sakamakon rawar da ya taka a matsayin Gus Fring a cikin shahararrun shirye-shiryen Breaking Bad da Better Call Saul.

0 Comment about the Post: