Saturday, June 20, 2026

Harin Isra’ila a Kudancin Lebanon Ya Kashe Mutane Biyar Bayan Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta

Harin Isra’ila a Kudancin Lebanon Ya Kashe Mutane Biyar Bayan Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta

Akalla mutane biyar ne suka mutu sakamakon wani harin jiragen saman Isra’ila a kudancin Lebanon, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnatin Lebanon suka bayyana, sa’o’i bayan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ƙungiyar Hezbollah.

Rahotanni sun ce jiragen yakin Isra’ila da jirage marasa matuka sun ci gaba da kai hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma kwana guda da ya wuce.

Wannan sabon rikici ya faru ne a daidai lokacin da wakilin Amurka kan harkokin diflomasiyya, Steve Witkoff, da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, suka nufi Switzerland domin tattaunawa.

Amurka ta bayyana cewa za a gudanar da sabon zagaye na tattaunawar Lebanon da Isra’ila a Washington daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Yuni.

Isra’ila da Hezbollah sun amince da tsagaita bude wuta ne bayan hare-haren jiragen saman Isra’ila da suka ratsa sassan kudancin Lebanon.

A gefe guda kuma, zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz ta ƙaru bayan yarjejeniyar da aka yi domin dakatar da rikicin Amurka da Iran.

Ana ci gaba da zaman dar-dar yayin da ƙasashen duniya ke ƙoƙarin hana ƙarin bazuwar rikici a Gabas ta Tsakiya.

0 Comment about the Post: