Tuesday, June 23, 2026

Ƙasashen Iran da Oman Sun Amince da Kafa Kwamitin Hadin Gwiwa Domin Gudanar da Mashigar ruwan Hormuz.

Ƙasashen Iran da Oman Sun Amince da Kafa Kwamitin Hadin Gwiwa Domin Gudanar da Mashigar ruwan Hormuz.

Kasashen Iran da Oman sun amince da kafa wani kwamitin hadin gwiwa domin tattauna yadda za su gudanar da muhimmiya Mashigar ruwan Hormuz, musamman batutuwan zirga-zirgar jiragen ruwa da ayyukan sufuri na teku da kuma kudaden da suka shafi wadannan ayyuka.

An bayyana wannan yarjejeniya ne a lokacin ziyarar Kakakin Majalisar Dokokin Iran Mohammad Bagher Qalibaf da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi zuwa Muscat, inda suka gana da Sarkin Oman Haitham bin Tariq da Ministan Harkokin Wajen Oman Badr bin Hamad Al-Busaidi.

A cikin wata sanarwa da kasashen biyu suka fitar, sun ce kwamitin zai kasance karkashin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu, kuma zai duba yadda za a tsara harkokin jigilar kayayyaki a Mashigar Hormuz da kuma ayyukan da suka shafi zirga-zirgar jiragen ruwa bisa ka’idojin kasa da kasa.

Iran da Oman sun kuma ce za su tuntubi sauran kasashen da ke kusa da mashigar da kuma sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna batutuwan da suka shafi wannan hanya mai matukar muhimmanci.

Kasashen biyu sun sake tabbatar da cewa suna goyon bayan tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz tare da mutunta dokokin kasa da kasa da kuma ikon kasashen da ke bakin tekun.

Oman ta kuma nuna goyon baya ga yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da hadin gwiwa.

Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai da kasuwanci a duniya, inda take hada Tekun Fasiya da Tekun Oman da sauran hanyoyin ruwa na duniya.

0 Comment about the Post: