Saturday, June 20, 2026

Ƙasar Ireland ta kori ’yan Afirka ta kudu 42 daga kasar wadanda ke zaune a ƙasar ba bisa ka’ida ba.

Ƙasar Ireland ta kori ’yan Afirka ta kudu 42 daga kasar wadanda ke zaune a ƙasar ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Ireland ta kori ’yan Afirka Ta Kudu su 42 da ake zargi suna zaune a kasar ba bisa ka’ida ba, inda aka mayar da su Johannesburg. 
Hukumomin Ireland sun ce an kashe kusan Euro 735,000 (kimanin dala 845,000) wajen gudanar da wannan aikin.

Rahotanni sun ce mutanen sun hada da maza 9, mata 18 da yara 15 da ke tafiya tare da iyalansu. 
An raka su daga filin jirgin saman Dublin a ranar Alhamis da jirgin haya na musamman, kuma sun isa Afirka Ta Kudu da safiyar Juma’a.

Wannan shi ne karo na hudu da Ireland ta gudanar da irin wannan korar baki a shekarar 2026.

Hukumar kula da shige da fice na ƙasar Ireland ce ta bayar da umarnin korar mutanen bayan an gano cewa suna zaune a kasar ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba su amince su koma kasashensu da kansu ba.

Mahukunta sun bayyana cewa biyu daga cikin wadanda aka kora suna da tsoffin laifukan da aka taba yanke musu hukunci a Ireland.

Duk da cewa Ireland na daukar Afirka Ta Kudu a matsayin kasa mai aminci, masu neman mafaka daga can dole ne su gabatar da hujjojin da ke nuna cewa suna fuskantar barazana kai tsaye idan za su samu damar zama.

Ministan Shari’a na Ireland, Jim O’Callaghan, ya ce tsarin shige da fice na kasar dole ne ya kasance mai tsauri kuma bisa ka’ida, domin tabbatar da amincewar jama’a.

Ya kara da cewa za a san cikakken kudin da aka kashe wajen aikin bayan an kammala biyan dukkan kudaden da suka rage.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun matsalolin shige da fice a duniya, inda wasu ’yan Afirka Ta Kudu ke fuskantar tsauraran matakai a kasashen waje, yayin da kasar Afirka Ta Kudu ita ma ke fama da matsalolin bakin haure marasa takardu da rikice-rikicen kyamar baki.

0 Comment about the Post: