Sunday, June 21, 2026

An Zubar da Kilogiram 1,802 na Tokar Takardun Alƙur’ani a Tekun Kudancin China.

An Zubar da Kilogiram 1,802 na Tokar Takardun Alƙur’ani a Tekun Kudancin China.

Hukumomi a jihar Sarawak da ke ƙasar Malaysia sun zubar da jimillar kilogiram 1,802 na toka daga kayayyakin Alƙur’ani da rubuce-rubucen da ke ɗauke da ayoyin Alƙur’ani a cikin Tekun Kudancin China kusa da ruwan Kuching.

An gudanar da wannan aiki ne a ranar Asabar, inda aka saka tokar cikin jakunkuna 212 na musamman masu kare muhalli (AQ-01) kafin a saki su cikin teku. Tokar ta samo asali ne daga aikin tsarkake kayayyakin Alƙur’ani da aka gudanar a cibiyoyin kula da su a fadin Sarawak.

Shugaban Sashen Alƙur’ani na Hukumar Addinin Musulunci ta Sarawak (JAIS), Abdul Rahim Rashid, ya ce wannan aiki wani bangare ne na shirin yau da kullum da aka tsara bisa shawarar Kwamitin Fatwa na Ƙasa, domin kare martabar kayayyakin Alƙur’ani da suka lalace bisa ka’idojin addinin Musulunci.

Ya bayyana cewa tsarin Sarawak ya bambanta da na wasu jihohi, domin suna amfani da jakunkuna na musamman masu narkewa a muhalli kafin a saki tokar.

A cewarsa, kowanne jaka yana ɗauke da kusan kilogiram 8.5, kuma an ƙera shi ne domin ya nutse sannan ya narke cikin ‘yan mintuna, ta yadda za a gudanar da aikin cikin tsari da mutuntawa.

An tattara tokar ne daga cibiyoyin tsarkake Alƙur’ani da ke Sibu, Sarikei da Kuching.

Bikin sakin tokar, wanda shi ne irinsa na farko mai girma a kudancin Sarawak, ya samu halartar jami’an addini, hukumomin ruwa, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

JAIS ce ta shirya shirin tare da haɗin gwiwar hukumomi da dama, ciki har da Hukumar Kula da Kogunan Sarawak, Rundunar ‘Yan Sandan Ruwa, Hukumar Kamun Kifi da Hukumar Kula da Tekun Malaysia.

A gefe guda, Majalisar Addinin Musulunci ta Sarawak ta ce cibiyoyin kula da kayayyakin Alƙur’ani na fuskantar matsin lamba saboda karuwar buƙata, inda ta yi kira ga a samar da ƙarin cibiyoyi domin ci gaba da kare darajar Alƙur’ani.

0 Comment about the Post: