Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenie ya bayyana cewa hadin kai mai karfi da ‘yan Iran suka nuna ya haifar da gagarumin tasiri, inda ya ce hakan ya raunana kokarin makiya.
Ya bayyana a wani sako da ya wallafa cewa hadin kan al’ummar ƙasar ya sa makiya sun shiga rudani da rashin tsari.
Jagoran ya kuma jaddada cewa dole ne a ci gaba da karfafa wannan hadin kai domin kare kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula da yakin farfaganda a yankin.
Tags
Labaran Duniya
