Sunday, April 19, 2026

Donald Trump ba shi da hakkin hana Iran 'yancin da dokar ƙasar da kasa ta bata game da Shirin Nukiliyar - Inji Shugaban Ƙasar Iran Masoud Pezeshkian.

Donald Trump ba shi da hakkin hana Iran 'yancin da dokar ƙasar da kasa ta bata game da Shirin Nukiliyar - Inji Shugaban Ƙasar Iran Masoud Pezeshkian.

Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce shugaban Amurka Donald Trump ba shi da wani haƙƙi na hana Iran “Mallakan nukiliya na zaman lafiya da doka ta bata”, 
Inda ya jaddada cewa Iran ba ta neman faɗaɗa yaƙi, kuma tana aiki ne kawai domin kare kanta.

“Shugaban Amurka yasha fadan cewa Iran kada ta yi amfani da haƙƙin ta na nukiliya, amma ba ya bayar da amsa kan laifin da muka aikata,” in ji Pezeshkian. 
“Shi wane ne shi da har zai hana wata ƙasa haƙƙin da doka ta ba ta?”

Ya kuma ƙara da cewa: “Iran ba ta neman faɗaɗa yaƙi ba, kuma ba ta fara wani rikici ba, kuma ba za ta fara ba. 
Ba mu kai hari kan wata ƙasa ba, kuma a halin da ake ciki ba mu da niyyar kai hari ga kowa. Muna aiki ne kawai wajen kare kanmu bisa doka.”

A lokacin rikicin, Iran ta kai hare-hare a yankuna daban-daban, ciki har da Bahrain da Kuwait, Oman da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Saudi Arabia da Syria da Iraq da Turkey day yankin Birtaniya na ketare Akrotiri da Dhekelia, da Yammacin Kogin Jordan (West Bank). Haka kuma an ruwaito wasu ayyuka a Azerbaijan.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: