Thursday, September 18, 2025

SAUKAKEN FASSARAR AL-KUR'ANI for Android V3.2.3

SAUKAKEN FASSARAR AL-KUR'ANI for Android V3.2.3

Manhajar Fassarar Al'kur'ani Mai girma da harshen Hausa

SASSAUQAR TARJAMAR MA'ANAR AYOYIN ALQUR'ANI MAI GIRMA CIKIN HARSHEN HAUSA.

JIZI'IN NA 30 (HIZIFI BIYAR)

Ina farawa da sunan Allah wanda ya shimfixa ni'marsa ga kowa da kowa a duniya, wanda ya keve bayinsa nagari da ni'imomi a lahira. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta annabi muhammadu da ahalul baitinsa.


Bayan haka. Assalamu alaikum xan'uwa Musulmi mai girma.

Wannan wani qoqari ne da ake yi na sauqaqa fahimtar ma'anar ayoyin Alqur'ani mai girma ga masu karanta harshen Hausa a duk inda suke.Sannan kuma, mun dogara ne tafsirin Almizan na Allama Xabaxaba'i da kuma darrusan tafiri na Ayatullahi Jawadi Amuli wajen xauke ma'anar ayoyin.

Wannan wani qoqari ne da muka faro shi don ganin an sauqaqa wa mutane musamman matasa da yara hanayar da za su shaqu da littafin Allah mai gairma, wato Alqur’ani mai tsarki a lokacin da suke karanta shi, kuma muna nemam shwarwari da tsokaci kan yadda aikin zai inganta don sauqaqa wa masu karatu xin, saboda haka, kai ma xan'uwa mai karanta waxannan shafuka a halin yanzu, muna roqon ka gudummowa wajen inganta wannan aikin ta hanyar ka karanta ka ji cewa ka fahimci abin da ake so a isar daga saqon ayoyin da ka karanta, ko kuwa ka fiskanci wani saqo na ayoyi ko wata aya da ba ka fahimci abin da ke ciki ba? 

Idan ka sanar da mu yadda ka fahimta sai kuma ka bayyana mana ra'ayinka kan yadda za a yi don a sauqaqa wannan saqo da ya shige maka duhu, ta hanayar sauya kalmomi ne, ko sauya tsarin jimlar ne ma baki xaya; musaman ma idan aka yi la'akari da cewa yara qanana ma suna karanta waxannan surori da ke cikin azu biyu kamar yadda abin yake a qasar Hausa!


Download and Install this App (8.3MB)

Install from Google Play 

Category

Education App 

Developer

ushibawiyyu initiative

Last Update

19 September, 2025

Version Requirement

Minimum 5.0+

Application Version

3.2.3

Application Size

8.3MB


SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: