A Musulunci, ranar kiyama, wanda aka fi sani da ranar sakamako ko kuma ranar karshe, lamari ne mai muhimmanci da ke nuna karshen duniya da mafarin Lahira.
An yi imani cewa a wannan rana ce, Allah madaukakin sarki zai tayar da dukkan mutane tun daga kan Wanda ya fara mutuwa har zuwa wanda ya mutu na karshe, domin a yi musu hisabi gwargwadon ayyukansu a rayuwar duniya.
Saboda da muhimmacin ranar Alkiyama sai da Allah madaukakin sarki ya saukar da Surah kacokan wacce ta ke Bayani dalla-dalla game da tashin kiyama.
Sai dai sanin ranar tashin kiyama Allah madaukakin sarki ya bar ma kansa ilimin sanin hakan shi kadai duk da cewa da yawan malaman Addinnin musulunci sun yi imanin cewa babu wani gaibu da Allah (S.W.T) bai sanar da Manzon Allah (S.A.W) ba sai dai ba'a umurce shi ya sanar ba, face Alamomin tashin kiyama kamar yadda yazo a hadisai mabanbanta.
Ga wasu daga cikin Alamomin tashin kiyama.
1. Mutane zasu wulakantar da Sallah.
2. Mutane zasu yawaita cin amanar junansu.
3. Qarya zata zama kamar ado awajen jama'a.
4. Yawaitar kisan-kai abisa kananan dalilai.
5. Za'a samu yawaitar cin kudin ruwa.
6. Akwai yawaitar dogayen gine-gine.
7. Mutane zasu wulakantar da 'Yan uwansu na
Zumunci.
8. Adalci zai yi Qaranci.
9. Jahilcin addini zai yawaita.
10. Mutane zasu sayar da addininsu akan 'Yan
kudade Qalilan.
11. Qarya zata zama kamar gaskiya awajen
mutane.
12. Yawaitar tufafin Alharini.
13. Zalunci zai yawaita.
14. Sakin aure zai yawaita.
15. Za'a yawaita Mutuwar gaggawa.
16. Maciyan amanar al'ummah su zasu zama
kamar masu Mutunci da amana awajen
al'ummah.
17. Za'a dauki masu Amana kamar sune
Maciyan amanar.
18. Za'a Gaskata Maqaryata
.
19. Za'a Qaryata magaskata.
20. Yarfe da Qazafi zasu zama ruwan dare.
21. Za'ayi matsanancin zafi duk da ruwan
sama.
22. Mutane zasu rika Qin haihuwa.
23. Mutane masu mummunan Asali, su zasu
zama cikin rayuwar jin dadi.
24. Mutanen kirki ne zasu tagayyara.
25. Masu amana zasu lalace su zama amciyan
amana.
26. Za'ayi azzaluman shugabanni.
27. Za'a samu yawaitar Malamai da Alkalai
Mazinata.
28. Mutane zasu rika sanya tufafin fata.
29. Zukatan al'umma zasu lalace
.
30. Zinare zai yawaita ako ina.
31. Za'a yawaita neman Azurfa.
32. Zaman lafiya zai yi Qaranci.
33. Zunubi zai yawaita.
34. Za'a yawaita yin ado da ayoyin Alqur'ani.
35. Za'a yawaita Qawata Masallatai da ado.
36. Za'ayi dogayen Hasumiyar masallatai.
37. Amma zukatan mutanen babu komai na
alkhairi aciki.
Allah madaukakin sarki ya bamu ikon cikawa da Imani mu tashi da Imani a Ranar Alkiyama don alfarman Shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W).
0 comments: