Hakika ilimi ginshiki ne dake gina rayuwar dan Adam, haka zalika rashin ilimi ga mutum tamkar gini ne da aka yi shi akan tubalin toka.
Annabi (S.A.W.) ya ce: "Neman ilimi wajibi ne a kan dukkan musulmi da musulma". Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye wajen neman ganin mun sami ilimin da za mu bauta wa Allah Madaukakin Sarki, domin kuwa Yana cewa ka san ni kafin ka bauta min.
Don haka matukar mutum yana raye neman ilimi a gare shi ba ya karewa na addini ko na zaman duniya domin cin ma wasu buƙatu na rayuwa, kamar su sanin kimiyya ko fasaha da makamantan su.
An karbo Hadisi daga Anas dan Malik Allah ya yarda da shi ya ce: "Na ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: Mai neman ilimi shi ne mai neman rahama, kuma neman ilimi yana daga cikin rukunan musulunci". Dailami shi ne ya ruwaito.
Wannan Hadisi yana nuna mana cewa rahama ba ta samuwa sai an samu ilimin nemanta a duniya, kuma shi kansa musulunci ba ya yiwuwa ga mutum sai yana da ilimin bautar Allah.
Haka ita kuma rayuwa takan tafi a hagungunce ne ga jahili wanda ba shi da ilimin sanin yadda duniya da lahira ta dosa da kuma yadda za'a sami zama lafiya a nan duniya da ranar gobe ƙiyama.
An karbo daga Anas Dan Malik Allah Ya yarda da shi ya ce: "Annabi (S.A.W.) ya ce, mafi tsananin hasara ga mutane ranar tashin ƙiyama su ne mutum wanda yana yiwuwa a duniya ya nemi ilimi bai nema ba, da mutumin da ya sanar da ilimi bai yi aiki da shi ba". Dan Askar ya ruwaito Hadisin.
Wajibi ne ga dukkkan musulmi ya tashi haiƙan tun yana kuruciyar sa ya nemi ilimin bautar Allah ba sai rayuwar sa ta kusa zuwa ƙarshe ba, wato lokacin da ya tsufa ya kasance yana mai danasani ko kokarin neman ilimi ba.
Domin ita rayuwa tana da dama mai yawa, amma idan mutum ya bari damarsa ta neman ilimi ta kubce masa to daga ƙarshe ko ya tashi neman ilimin sai ka tarar yana yi masa wahala.
Zamu kara fahimtar muhimmacin ilimi ga rayuwar musulmi idan muka duba yadda fiyayyen Halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam ya nunar a cikin wadannan hadisan.
Anas bn Malik ya ruwaito cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Neman ilimi wajibi ne akan kowane musulmi."
طَلَبُ الْعِلْمِ فَرِيضَةٌ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ
[Sunan Ibn Mājah 224]
Haka zalika a cikin wani hadisin:
Abu Huraira ya ruwaito cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللَّهُ لَهُ
بِهِ طَرِيقًا إِلَى الْجَنَّةِ وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللَّهِ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ إِلاَّ نَزَلَتْ عَلَيْهِمُ السَّكِينَةُ وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ وَحَفَّتْهُمُ الْمَلاَئِكَةُ وَذَكَرَهُمُ اللَّهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ
"Duk wanda ya bi hanyar neman ilimi, Allah (S.W.T) zai sauqaqa masa hanyar shiga Aljannah.
Mutane ba sa taruwa a cikin dakin Allah, suna karanta littafin Allah kuma suna karantar da shi tare, face sai natsuwa ta sauka a gare shi, rahama ta lullube su, mala'iku su kewaye su, kuma Allah Ya ambace su ga na kusa da shi". [Sahih Muslim 2699]
Hakika da wadannan hadisin zamu fahimci cewa neman ilimi wajibi ne ga duk musulmi domin yana da tarin falalar da babu wanda yasan iyakarshi sai Allah madaukakin sarki.
Ya Allah Ka ƙara mana ilimin bauta maka da sanin halin rayuwa, Allah Ka sa mu cika da imani da kalmar shahada, Ameen summa Ameen.
0 comments: