Sunday, June 22, 2025

Yadda ake yin salatul tasbihi

Yadda ake yin salatul tasbihi

Sallar tasbihi Sallah ce wanda akeyin raka'a 4 da nufin neman gafaran Allah madaukakin sarki daga zunuban da mutum ya aikata.
Annabi Muhammad (S.A.W) yace duk wanda yayi wannan sallah ana gafarta ma shi zunubansa na baiyane da na boye tun daga haihuwarsa har zuwa lokacin da yayi wannan sallar kamar yadda ya zo a cikin hadisi.
Kuma yace ya kamata kowane musulmi yayi kokarin yin wannan Sallar a kullum, in bai samu iko ba ya yita a cikin mako/sati, ko wata, ko acikin shekara ln kuma bai samu dama ba yayi ta acikin rayuwarsa ko da sau daya ne.

GA YADDA AKE YINTA

Raka'a ta farko
Ana karanta fatiha, da surah kafin ai ruku,u sai a karanta wadannan tazbihin:

SUBHANALLAHI sau 15
WAL HAMDULILLAHI sau 15
LA ILAHA ILLALHU sau 15
WALLAHU AKBAR sau 15

* Idan anyi ruku'u sai a sake karanta wadannan tazbihin sau 10
* Idan an taso daga ruku'a kafin sujjada a karanta sau 10
* Idan anyi sujjada a karanta sau 10
* Idan an taso daga sujjada a karanta sau 10
* Idan an koma sujjada a karanta sau 10
* Idan an mike raka'a ta biyu a sake karanta

SUBHANALLAHI
WAL HAMDULILLAHI
WA LA'ILAHA ILLALLAHU
WA ALLAHU AKBAR sau 15 kamar yadda mutum yayi a raka'ar farko, 
(Wato bayan ko wace fatiha da surah mutum zai karanta tazbihin sau 15, 
Bayan ruku,u da sujada sau 10.
Haka za'ayi dukkan raka'oin guda 4.

Idan mutum ya ga dama zai iya yin sallama 1,  idan kuma ya ga dama zai iya yin sallama 2.
Duk Wanda mutum yayi ya inganta

Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yi.


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: