Ranar Arfa Rana ce Mai matukar muhimmanci da tarin falala ga musulmi, ko da kuwa mutum baije hajji ba.
Addu'ar ranar Arfa ita ce mafi alherin addu'o'i kamar yadda manzon tsira Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su Kara tabbata a gare shi yace a wannann Hadisin da Imam Tirmizi ya ruwaito.
Manzon Allah (SAW) Yace: "Mafi alherin addu'a ita ce addu'ar
ranar Arfa, kuma mafi alherin abinda
na fada ni da Annabawan dake
gabani na shine...
"LA ILAHA ILLALLAHU
WAHDAHU LA SHAREEKA LAHU,
LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADEER."
0 comments: