Tuesday, April 22, 2025

Tarihin Annabi Musa (As)

Cikakken Tarihin Annabi Musa (AS)

Annabi Musa AS Yana daga cikin Annabawan Allah ulul azam guda biya Kuma shine Annabin da Allah ya aiko shi izuwa ga babban kafiri Fir'auna.

NASABARSA

Annabi Musa ya fito daga cikin Banu Isra'ila. Sunansa Musa Ibn Imran Ibn Lahib Ibn Gazir Ibn Lawiy Ibn Ya'akub Alaihissalam, kuma babu shakka a nasabar tasa inji "Ibn Hajar Al askalani". Anyi sabani a kan sunan mahaifiyarsa; ko Baduna ko Abazakit ko kuma Yuhanid.

GIDAN FIR'AUNA

Fir'auna ya ga a cikin mafarki wata wuta ta taso tun daga Baitul Makaddis ta kone gidajen "Misra" baki daya, amma ban da gidajen Banu Isra'ila. Da ya farka daga barci sai ya tara bokaye da 'yan sihiri, sai suka ce masa ai wani yaro za a haifa daga cikinsu kuma shi zai yi sanadiyar rushewar Misra. Fir'auna sai ya yi umarni duk yaron da aka haifa daga cikinsu a kashe.

HAIFUWAR ANNABI MUSA

Lokacin da aka haifi Annabi Musa sai Allah ya umarci mahaifiyarsa ta shayar da shi, duk lokacin da kuma ta tsorata ta jefa shi cikin kogi. Daga nan sai ta ke shayar dashi amma duk lokacin da ta ji tsoran za a ganeta sai ta jefa shi cikin wani akwati a kan ruwa amma ta daure shi a gabar kogin da igiya.

Watarana sai ta manta wannan igiyar ta jefa shi kogi ya tafi da shi bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan Fir'auna. Bayi suka tsinceshi suka kai shi wa Asiya matar Fir'auna, ta bude akwatin sai ta ga kyakkyawan yaro, sai ta nemi Fir'auna ya bar mata shi kuma ya bata shi ta reneshi.

Umman Musa kuma na can hankalinta ya tashi babu abin da take tunani sai Musa. Tana sane alkawarin Allah gaskiyane, Musa dai bai nitse cikin ruwa ba. Daga nan sai ta umarci yayar Musa ta fita neman labarinsa.

Ta same shi gidan Fir'auna kuma ta nemi izini ta nuna musu gidan da za a kai shi shayarwa a biyasu kuma suka yarda. Allahu Akbar! Musa ya dawo wajen mahaifiyarsa ta ci gaba da shayar dashi kuma ana biyanta, iko sai Allah mai yin abin da ya ga dama.

KISAN ABOKIN GABA

Annabi Musa ya taso har ya girma. Wata rana yana tafiya kan hanya a cikin gari, sai ya samu wasu mutane biyu na fada, daya daga Banu Isra'ila dayan kuma daga kabilar Fir'auna. Da Banu Isra'ila ya ga Annabi Musa sai ya nemi taimakonsa kasancewar kabilarsu daya kuma Fir'aunawa sun kasance suna zalintarsu. Annabin Allah Musa ya je taimakon dan uwansa sai ya kashe abokin gaba bisa kuskure. Daga nan sai ya kasance yana yawo cikin gari a tsorace.

Wata rana kwatsam yana yawo sai ya ji wancan dan uwan nasa yana sake neman taimakonsa suna fada da wani. Annabi Musa ransa ya fusata yake ce da shi amma kai ka fiye husuma, yayi yunkurin cetonsa shi kuma ya tsorata ya dau shi zai aukawa. Daga nan sai cewa yake: Nima kar ka kasheni kamar yadda ka kashe wancan.

Labari ya watsu cikin gari kamar wutar daji Annabi Musa ne ya kashe mutumin nan da ba a san wadda ya kashe shi ba. Fir'auna ya tara 'yan majalisa a ka yanke wa Annabi Musa hukuncin kisa.

HIJJIRA DAGA MASAR

Wani mutum mai imani cikin 'yan majalisar fir'auna ya sulalo ya sanar da Annabi musa halin da ake ciki kuma ya ba shi shawarar ya gudu ya bar Misra. Nan da nan Annabi Musa ya fita a tsorace.

BAKUNTA A MADYANA

Bayan tafiya mai nisa da wahala da gajiya ya isa wani gari da ake ce da shi Madyan.

Isar sa ke da wuya sai ya ga mutane da dabbobinsu na shayar da su ruwa, a can gefe guda kuma ga wasu mata nan guda biyu suna jiran mazajen nan su gama su kuma sai suma su shayar dabbobinsu. Da ya ga haka sai ya tambayi 'yan matan me ya sa hakan, suka sanar da shi ba sa cudanya da maza ne shi ya sa sai sun gama kuma babansu tsoho ne a gida ba zai iya aikin ba. Hakan ya birgeshi kuma sai ya je ya shayar musu da dabbobin nasu suka kora suka tafi gida.

Da isarsu gida, babansu ya yi mamakin dawowarsu gida da wuri ba kamar yadda suka saba ba. Ya tambaye su dalili suka sanar da shi wani mutum ne ya shayar musu dabbobin. Da tsoho ya ji haka sai yace dayarsu ta kira Annabi Musa.

......Zamu cigaba InshaAllah 


Article Translation in English Language.

Prophet Musa AS is one of the five most honorable Prophets of God, and he is the Prophet that God sent to the great infidel Pharaoh.




SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: