Tuesday, April 22, 2025

Wacece Fatima bint al-Khattab (RA)?

Wacece Fatima bint al-Khattab (RA)?

Fatima bint al-Khattab Sahabiyar Manzon Allah (S.A.W) ce Kuma kanwar Umar Ibn Al-Khattab (RA) da Zaidu bn al-Khattab (RA). Wacce ta sanadinta Sayyidina Umar bin kattab ya karbi musulunci.

Ita ce 'yar auta a wajen mahaifinsu Khattab bn Nufayl wanda ya aurar da ita ga Sa'id bn Zaid (RA). Fatima tare da mijinta duk sun musulunta a lokaci guda.

Ita ce Fatima bint al-Khattab bn Nufail bn Abdil Uzza, ta taso a daya daga cikin manya-manyan gidajen Quraishawa na Makkah. Ta shahara a matsayin wadda ta fuskanci babban makiyin Musulunci a lokacin, ta mayar da shi abin koyi.


Ta auri Sa'eed Ibn Zaid daya daga cikin sahabbai goma da aka yi musu bushara da Aljanna. Zaid bn Nufail mahaifin Sa'eed shi ne mutumin da ya kasance yana ceto matan da aka haifa daga binne su da rai, kuma yakan ce wa duk wanda yake son ya kashe 'yarsa, kada ka kashe ta. Zan biya kudin renonta. 


Sa'eed ya karbi Musulunci a hannun wani sahabi mai daraja, Khabbab Ibn al-Arat (RA). Bayan ya yi shelar yin imani da Annabi (SAW) ya koma wurin matarsa ​​Fatima ya ba ta labarin sabon imanin. Wannan mace mai martaba ta yi saurin fahimtar gaskiya kuma ta karɓi bangaskiya.


Dukkansu biyun sun boye imaninsu ne saboda tsoron fitina, musamman a hannun dan’uwanta Umar, wanda a lokacin yana cikin bata ya yi kokarin kawar da Musulunci daga Makka da kashe Manzon Allah (SAW). Haka kuma Khabbab ya kasance yana yawan zuwa gidansu yana karantar da su Alqur'ani da Musulunci. 


A lokacin ne Umar ya fusata da yaduwar Musulunci, ya yanke shawarar kawo karshensa gaba daya. Ya dauki takobinsa ya nufi gidan Arqam, wanda shi ne wurin da Manzon Allah (SAW) yake wa’azin imani ga muminai. Ya yi niyyar kashe Annabi (SAW). Yana cikin tafiya sai wani daga cikin mutanen Bani Makhzum ya tarye shi, yana ganin mumunan fushi a fuskarsa ya tambaye shi, "Ina za ka?" Sai Umar ya ce: “Zuwa ga Muhammad bn Abdullah! Ina so in kashe shi, in kwato Larabawa daga addininsa!”

Sai mutumin ya ce masa, “Shin kana tsammanin dangin Abd Manaf za su bar ka idan ka kashe shi? Ka fara maganin na  gidan ku tukuna.”

Umar ya tambaya cikin tsananin mamaki da tsananin fusata, “Me kake nufi? Wa kake nufi?


Sai mutumin ya amsa da cewa, baka sani ba, ‘Yar uwarka da surukinka duk sun musulunta kuma sun bi Muhammad (SAW).


Jin haka Umar ya canza hanya ya nufi gidan yar'uwarsa. Yana isa gidanta sai yaji ana karanta wasu ayoyin alqur'ani wanda bai gane ba. Ya buga da karfi ya daka wa Fatima tsawa ta bude kofar.


Jin haka shi yasa Khabbab yayi sauri ya boye a wata kusurwar gidan, Fatima ta ajiye fatun da suke koyon alqur'ani a jiki. An ce suna karanta ayoyin Suratu Ta Ha ne. Sannan ta bude masa kofa. Ya tambaye ta sautin da yakeji da tsoratar dasu game da amincewarsu da sabon Addinin da kuma sakamakon da zai biyo baya idan hakan ya kasance. Anan ne Fadima tayi karfin hali ta fito ta fuskanci dan uwanta. Ta fad'a masa da k'arfi, cewa sun musulunta ita da mijinta sun sheda cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu (SAW) manzonsa ne.

Jin haka daga bakin 'yar uwarsa yasa Umar ya fusata har ya kai ya buga kan Sa'eed a jikin bango. Fatima na ganin haka sai ta mike don kare mijinta, ta tsaya a tsakanin mutum biyu, Umar ya doke ta akai har sai da ta fara zubar da jini. Daga nan tsoro ya gushe daga gare su gaba daya, suka ce, ‚Lallai haka ne, mu zamo Musulmai! Ka aitaka dukkan abin da kake son aikawa.‛ Saboda nuna rashin tsoron da suka yi ga Umar kuma ya ga kan ‘yar uwansa na zuban jinni sai ya fita. Daga baya ya koma ya roki ‘yar uwansa da ta nuna mashi fatun wadda ita da mijinta suke karantawa tare; bayan ta mika mashi takardun, sai ya karanta nan take fuskarsa (kamanninsa) ta fara canzawa saboda bakin cikin abin da ya aika ta. .

Da ya kare karatun nan sai ya firgita, firgita mai tsanani saboda kyawon abin da ya karanta da martabarsa kuma da abin da yake koyarwa, da kuma tasirin abin da sakon ya kunsa. Daga nan Umar tunaninsa mai kyau ya fara gaya mashi gaskiya. Sai ya bar gidan ‘yar uwansa, zuciyarsa tana cike da dogon tunani. Kuma ransa ya fara darsa mashi yarda da sabon ban gaskiya da bayyanar shi gare shi; sai ya tafi kai tsaye zuwa ga Saffahin da Annabi Muhammad (SAW) yake ganawa da mabiyansa, don neman yanda zai shiga wannan addinin. 

Nan take Umar ya bayyana karban musuluncinsa a gaban Annabi (SAW). Musulmai sun yi farin ciki da mamaki game da shigar shi Musulunci saboda karin karfin da suka samu ga Hamza, kuma ga wani sabon tsaro ya karu cikin al’umma ta gaba daya. Musuluntar Umar ya kara raba kan kuraishawa fiye da yadda suke a baya, kuma hakan ya rage musu karfi kuma ya rage musu samun matsayin gudanarwa. Kuma haka ya kara wa Musulunci karfi babba; kuma haka ya sanya shi (Musulunci) tasiri wanda su da kuraishawa ko wane zai kara canza matsayinsa.

Haka ya samar da wata sabuwar hanya na gudanar da addini kai tsaye da kuma sadaukarwa da sabon tsaro ga dukkan wadanda suka yi kaura ga Annabi Muhammad (SAW). Nan take bacin ransa ya kau aka tada bangaren mutuntaka. Kamar yadda Allah ya so sai ya tambayi kanwarsa game da abin da suke karantawa. Ta roke shi da ya tsarkake kansa, ya yi alwala kafin ta bar shi ya taba takardan da ke dauke da ayoyin Alqur'ani mai girma.

Da haka ne a gidan Fatima da Sa'eed, Umar ya sake wani sabon ganye. Allah (SWT) ya karrama su duka, ya zabe su a matsayin tushen shiriyar Umar zuwa ga Musulunci. Fatima ce ta fuskanci Umar ta canza yanayin rayuwarsa.

Allah ya kara yarda da Fatima bint al-Khattab. Domin lallai Allah Ya zabe ta ta zama hanyar da dan uwanta ya karbi Musulunci.

Article Translation in English Language.

Fatima bint al-Khattab was a companion of the Messenger of God (S.A.W) and the younger sister of Umar Ibn Al-Khattab (RA) and Zaid bin al-Khattab (RA). Which caused Sayyidina Umar bin Kattab to accept Islam.




SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: